Kannywood

Duk abun da ya samu adam zango wannan aminu j town din ya taka babbar rawa wajen saka adam zango a damuwa

Wani matashi mai amfani da kafar sada zumunta Farouq Abdullahi Tukuntawa shine ya fadi irin abubuwan da Aminu j town ya haddasa wajen bada gudumuwa wajen cin mutuncin da shiga yanayin da adam a zango yake ciki.

Inda yake cewa.

Ba lallai bane don Allah ya baka baki da zakin murya da kuma wadanda suke sauraronka ka fito ka dinga kunnawa bawan Allah wuta ba

Tun baya kula ka har ka jawo dole sai ya kula ka

Chin mutunchi a social media ba kowane yake da zuciyar da zai iya jurewa ba

Wlh akwai wanda iya comment kawai na mutane a media zai iya sawa ya hadiyi zuciya ya mutu

Mutane da yawa bawai magana ne bazasu iya a media ba a’ah maganganun mutane shine damuwar su

Wani nan da nan sai ya goga maka maganar da zakayi shekara tana chinka a zuciya shi kuma a yan sakanni ya fada maka yayi wucewarsa ba abubda ya masa zafi

Ballantana wanda zai zo yau yayi video akanka gobe ya karayi jibi ya karayi don kawai ya bata ka

Musamman kuma kaga mutane suna yarda da abun da yake fada suna zaginka suna juya maka baya

Mu kanmu lokachin da akayi wata guguwa anan Facebook mun shiga damuwa kwarai da gaske ga duk wanda yayi posting ya zagemu domin saukakawa kanmu munyi blocking din mutane da bamu san adadi ba kuma munji zafin yadda wasu da muka sansu suka sanmu suka juya mana baya a lokachin suka kasance suna goyawa masu zaginmu baya duk yadda muke dasu haka muka hakura muka yanke alaqar mu dasu muka sharesu daga cikin rayuwar mu muka manta dasu mukachi gaba da rayuwar mu da mun chigaba da zama dasu da haka zasuyi mana illa su sa mana damuwar da kudi ma ba lallai ya iya mana magani ba

Wlh mu kiyayi kalmomin mu akan mutane domin wasu kalaman guba ne wlh iriin illar da sukewa mutane ba kadan bane but mu muna ganin ai kawai comment ne ba lallai yayi tasiri akan wanda muka fadawa ba

Wani inka ganshi a media to duniya ce ta masa zafi yazo ya rage zafi yayi abu kazo da mummunan baki ka soka masa magana ka wuce baka san irin illar da maganar ka zata masa ba

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button