Labarai

Hotuna : Yar chiko da ta kubuta daga hannun yan Boko Haram tayi wuff da wani bature a Amurka

Advertisment

Joy Bishara, daya daga cikin ‘yan matan makarantar da ta tsere bayan Boko Haram ta kai hari makarantar Sakandaren Gwamnati da ke garin Chibok a Jihar Borno, a shekarar 2014, kwanan nan ta samu masoyin da suka yi baiko da juna a Kasar Amurka.

Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Kimanin dalibai mata 276 ‘yan shekaru 16 zuwa 18 ne kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da su saga Makarantar Sakandaren Mata ta Gwamnati da ke garin Chibok a Jihar Bornon Najeriya.

‘Yan mata 57 daga cikin ‘yan matan sun tsere nan take bayan faruwar lamarin inda suka yi tsalle daga manyan motocin da ake jigilar su.

Karin wasu yan matan sojojin Najeriya ne suka ceto su amma sama da 100 sun bata.

Duk da haka, Bishara da dan uwanta, Lydia Pogu, wadanda suna cikin wadanda suka tsere daga harin da ya dauki hankalin duniya, sun koma Amurka.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Ta kamma karatu daga Jami’ar Kudu maso Gabas, inda ta sami digiri a aikin zamantakewa a shekarar 2021.

Bishara kwanan nan ta samu masoyi wanda suka yi baiko a Amurka. A ƙasa akwai hotuna.

Hotuna : Yar chiko da ta kubuta daga hannun yan Boko Haram tayi wuff da wani bature a Amurka Hotuna : Yar chiko da ta kubuta daga hannun yan Boko Haram tayi wuff da wani bature a Amurka Hotuna : Yar chiko da ta kubuta daga hannun yan Boko Haram tayi wuff da wani bature a Amurka Hotuna : Yar chiko da ta kubuta daga hannun yan Boko Haram tayi wuff da wani bature a Amurka Hotuna : Yar chiko da ta kubuta daga hannun yan Boko Haram tayi wuff da wani bature a Amurka Hotuna : Yar chiko da ta kubuta daga hannun yan Boko Haram tayi wuff da wani bature a Amurka Hotuna : Yar chiko da ta kubuta daga hannun yan Boko Haram tayi wuff da wani bature a Amurka

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button