Kada Mutum ya bari wani matsayi na wucin gadi yasashi kasa fadin Gaskiya ~Hadimin da Gwamna Ganduje ya dakatar
Hadimin gwamnan Kano, Salihu Tanko Yakasai da gwamnan ya dakatar saboda dukar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa kada mukamin wucin gadi yasa mutum ya kasa goyon bayan Abinda Al’umma ke so.
Ya Rubuta a shafinsa na sada zumunta cewa ko me kake a Rayuwa kada ka sake ka kasa bayyana ra’ayinka. Ka yi magana akan rashin gaskiya da kuma rashin adalci. Ka nemi hakkinka kuma kada ka bari mukamin wucin gadi yasa ka kasa goton bayan Abinda al’umma ke so.
Whatever u do in life, make sure u never lose ur voice. Speak up against injustice, speak up against inaction, speak up for what u believe in, demand for ur right and never let a temporary position or privilege stop u from standing with the people. Enough is enough! #EndSARS
— Peacock (@dawisu) October 11, 2020