Labarai

Yanda Na Sayawa Shugaban Yan Bindiga Motar Yaki akan miliyyan N28.5M -Musa kamarawa

Yanda Na Sayawa Shugaban Yan Bindiga Motar Yaki akan miliyyan N28.5M -Musa kamarawa Na taba sayawa Dan bindiga kachalla halilu tubali Wanda akafi sani da suna Halilu sububa motar yaki akan kudi N28.5m.
Musa Kamarawa aboki Kuma Mai yiwa hatsabibin shugaban yan bindiga bello turji safarar makamai yace akwai lokacinda ya taba sayowa halilu tubali shugaban yanbidigar yammacin Africa motar yaki
Yana wannan bayanine agaban mataimakin shugaban yan”sanda maikula da operation, Zaki Ahmad ranar litinin.
Kamarawa yace akwai lokacinda yaje cotonou jamhuriyar Benin wajen sayen motar yakin ma kachalla, yaje Bai samuba Sai ya Kira Wani Mai Saida mota a Libya Wanda shi dillalin motocin na Libya ya bashi lambar wayar Wani mutum a jamhuriyar niger.
Bayan munhadu da wannan mutum na niger shine ya karbi kudi ya kawo mana wannan motar yaki nikuma na kaiwa kachalla Hali motar, Dan uwana Aminu shine yasan hanyar da yabi ya kaiwa kachalla Hali motar yakin a daji.
Munsayi motar akan kudi naira
N28.5 million, Amma Ina matukar Dana sanin hakan Kuma bazan Kara yin hakaba nakuma Yi alkawrin agazawa jami”an tsaro wajen kama duk Wani mai tada zaune tsaye inji musa kamarawa.
Mataimakin shugaban yan”sanda Zaki yace tuni yansanda suka baza komarsu da Shan alwashi Sai sun karbi motar yakin a duk Inda take.
Daga: Mustapha sarkin kaya.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA