Kannywood

Sana’a Goma: Ali Artwork ya buɗe kamfanin sayar da Motoci da cinikin Gidaje

Fitaccen tauraron fina-finan Hausa Ali Muhammad Idris, wanda aka fi sani da Ali Artwork, ya raba kafa inda ya bude wani kamfani a jihar Kaduna da birnin tarayya Abuja mai suna AliArtWork Enterprises.

Jarumin wanda fitacce ne a cikin fina-finan Hausa na kannywood, musamman harkar barkwanci ya bude wajen ne musamman domin samar da ayyukan yi ga matasa.

Ana gudanar da abubuwa da dama a wajen, kamar sayar da motoci da bayar da su haya da hada – hadar gidaje da filaye da kuma harkokin tuntuɓa.

A shafinsa na Facebook, Ali Artwork ya wallafa wasu daga cikin hotunan buɗe wajen, inda ya gayyaci ƴan uwa da abokan arziki domin su ta ya shi murna.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button