Kalli Shirin ALAQA Episode ORG – Ali Nuhu
Gari na wayewa masu aikin hotel sun shigo gyaran daki suka tsinci wata baiwar Allah cikin wani hali, an shayar da ita sannan an mata fyade. Hakan ya saka kowa cikin rudani don babu kowa a dakin sai ita kadai sannan bata cikin hayyacinta balle ta yi wani bayani da zai nuna yadda ta tsinci kanta a wannan halin…..!
Wa ke da ALAQA da halin da yarinyar nan ya tsinci kanta?
*Fyade
*Shaye Shaye
*Talauci
*Cin amana
*Fin karfi
*Cin Zarafi
*Yaudara
*Gabar cikin gida
Duk suna kunshe a ciki!
Sabon shiri daga kamfanin Alu nuhu wanda shiri ne na soyayya da ban tausayi da kuma abin alajabi.
Wannan sabon shiri ne da ali nuhu ya shirya wanda yasanya gwarazan yaransa yan bana.
Wanda tabbas wannan shirin shima zai taka rawar gani sosai a cikin wannan shiri mai suna ALAQA.
Ga shirin nan ku kalla daga tashar YouTube mai suna Ali nuhu .



