Labarai
Da duminsa: Barayi sun kai hari Aso Rock, sun yi yunkurin shiga gidan nakusa da Buhari


Advertisment
Labari da duminsa na nuna cewa wasu barayi sun yi yunkurin fasawa cikin gidan shugaban ma’aikatar fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, dake Aso Rock, birnin tarayya Abuja.
Kamar yadda Legit ta ruwaito Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki da yammacin Litinin.
Garba ya bayyana cewa barayin basu samu nasarar satan komai ba.
“Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, ya tabbatar da cewa an yi “wawan yunkurin” yi masa fashi a gidans misalin karfe 3 na daren nan amma basu samu nasara ba,” Garba Shehu yace.
“Farfesa Gambari…ya ce babu wani abin damuwa.”
