Ashe Dan Asalin Jihar Borno Da Ya Yi Nasara A Gasar Karatun Kur’ani Na Duniya A Kasar Saudiyya Iyayensa A Sansanin ‘Yan Gudun Hijira Suke Da Zama? (Hotunan)
Ikon Allah kenan, bawan Allah Hafiz Idris Abubakar da yazo na daya a gasar karatun Al-Qur’ani Maigirma na duniya na wannan shekarar (2019) da ya gudana a Kasar Saudiyya ‘dan gudun hijira ne.
An ce yanzu haka iyayensa ma suna da zama a sansanin ‘yan gudun hijira na Madinatu dake garin Maiduguri, ta’addancin Boko Haram ya koro shi tare da iyayensa daga garin Marte suka dawo Maiduguri a matsayin ‘yan gudun hijira.
Haka Allah Ya ke al’amarinSa, taron dangin makiya addinin Allah na duniya sun kalli jihar Borno cibiyar karatun Qur’ani a nahiyar Afirka, sai suka jibge kwangilar ta’addancinsu a gurin domin a rusa Musulunci a hana karatun Qur’ani
Ko a yanzu Allah Ya kunyata mummunan shirin da sukayi, ‘dan gudun hijira ya zama gwarzon Qur’ani na duniya a wannan shekara ALHAMDULILLAH kwangilar ta’addancinsu da batancinsu bai hana a koyi Qur’ani a Haddace ba
Yaa Allah Ka daukaka Musulunci da musulmai Ka kasantar da kafirci da kafurai. Amin.
Daga Datti Assalafiy