Abba Kyari yayi Nasaran Kama Gawurtattun Yan Ta’adda masu Kidnapping Mutum 48 (hotuna)


Jarumin ‘dan Sanda DCP Abba Kyari kwamandan rundinar Intelligence Response Team (IRT) ya samu nasaran kama gawurtattun barayi ‘yan ta’adda masu garkuwa da mutane mutum 48
A cikin ‘yan ta’addan akwai mutum 9 wadanda sukayi garkuwa da ‘dan majalisar jihar Tarana Hon Muhammad Bashir Bape, Abba Kyari ya kamasu daya bayan daya a maboyarsu dake Taraba da Pilato, ‘yan ta’addan kwarartu ne a harkan garkuwa da mutane a jihar Taraba da yankin Arewa ta tsakiya
Ga sunayensu kamar haka:
(1) Yusuf Abubakar ‘dan shekara 31
(2) Muntari Umar ‘dan shekara 27
(3) Ahmad Dahiru ‘dan shekara 28
(4) Ali Alhaji Wuringo ‘dan shekara 25
(5) Buhari Nuhu ‘dan shekara 25
(6) Muhammad Garba ‘dan shekara 30
(7) Yusuf Jibrillah ‘dan shekara 24
(8) Adamu Amadu (Bulala) ‘dan shekara 32
(9) Idi Suleiman



Akwai mutane 12 cikin wadanda Abba Kyari ya kama, su kuma sun kware ne wajen aikata miyagun laifuka a yanar gizo, shekarunsu bai wuce tsakanin 22 ba zuwa 30, an kamasu ne a yankin Kubwa dake babban birnin tarayya Abuja
Sannan Abba Kyari ya kama wani tsohon banza ‘dan shekara 61 mai sjna Musa Usman daga jihar Kebbi da wani mai suna Ahmed Shu’aobu ‘dan shekara 27 daga jihar Nasarawa wadanda su kuma aikinsj shine sayar da miyagun kwayoyi wa manyan barayin daji a sansaninsu dake Babuga jihar Nasarawa, tsohon yana amfani da tsohontakarsa wajen tsallake tarkon jami’an tsaro kafin daga bisani aka samu nasaran kamashi da kullin kwayar koken guda 35
DCP Abba Kyari sun kwato bindigogi guda 41 da bindiga kirar AK47 guda 14 a hannun ‘yan ta’addan, AK47 Magazines guda 10, harsashin Cartridges guda 40, harsashin AK47 guda 4, abin cire kudi POS guda 4, na’urar laptop guda 2, Wayoyi guda 18, Internet MODEM da kuma katin cire kudi ATM guda 9
Muna fatan Allah Ya kara wa DCP Abba Kyari taimako da nasara akan ‘yan ta’adda
Amin


