Labarai

Gobara ta kashe mutum 134 a Kano a 2020

Hukumar kashe gobara ta Jihar Kano ta ce mutum 134 ne suka rasa rayukansu a 2020 sakamakon gobara 786 da suka tashi a wuri daban-daban a jihar.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito Saidu Muhammad, mai magana da yawun hukumar, yana bayyana cewa kazalika an rasa dukiyar da ta kai naira miliyan 635 a tsawon shekarar.
 
 
 
Kamar yadda Bbchausa na ruwaito.Haka nan, hukumar ta ceto ran mutum 1,077 da kuma dukiya naira biliyan 2.56.
“Akasarin gobarar sun faru ne sakamakon ganganci wurin aiki da tukunyar gas da amfani da wayoyin lantarki marasa inganci,” a cewarsa.
Ya ƙara da cewa hukumar za ta ƙara horas da ma’aikatanta guda 350 a 2021 domin kyautata aiki kuma ya shawarci magidanta da “su riƙa kulawa da kyau yayin amfani da wuta” domin guje wa tashin gobara.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button