Uncategorized

IZNAH PART 8 : Labari Da Cike Da Makirci

Iznah *8*
Ja baya yayi da sauri cikin ‘dan 6ata fuska Yana qare musu kallo.
A ‘dan ladafce gwaggo tace,
Yi hakuri kamalu Bata lura dakai bane baquwace duk a takure take shiyasa.
Kallon ananon yayi tundaga sama har qasa Nan take idanuwansa suka kyallo Masa kyanta da dirinta dazai fita matuqar tasamu kyakkyawar rayuwa musamman dogon hancinta daya qarawa fulani face ‘dinta kyau da tsari.
Wani gajeran murmushin gefen baki yasaki tareda ‘dan sakin fuska ya maido kallonsa kan gwaggon yace,
Baquwar waye cikin gidan?
Washe baki gwaggo tayi tace,
Eh wlh ‘yatace ‘yar gurin yayana da muke uwa ‘daya uba ‘daya tazo guri nane Zan kaita ta gaida hajiya babba.
Wucewa yayi da sauri sbd Kiran daya shigo wayarsa Yana cewa,
Ki shiga idan nadawo xan gaisa da ita.
Murmushi gwaggo tayi sbd Sam kamalu yafi yayansa saheeb sakewa dason mu’amala da mutane Kuma gidan kaf yafisu rashin qyamar mutane Ammafa kaf yafisu rashin imani da tausayi Dan komai na uwarsa mum asee bai baroba.
Itadai Wani yawu Anano ta ha’diye daqyar tareda saurin sauke kanta qasa sbd wani kallo daya jefeta dashi daya mugun fa’dar Mata da gaba.
Da sallama suka shiga palon Nan Anano taga kyau da tsari tareda uwar dukiya na aka narka a palon ta sake sauke kanta qasa sbd itadai zuwa lokacin jitake Sam Zama a hannun gwaggon yafita ranta sbd yanda takejin fa’duwar gaba da wani irin tsoro irin yanda ta riqa ji lokacinda qaddarar samun abdulshakur zata sameta,.
Kicin gwaggo ta nufa gurin asabe suka gaisa tace,
Ga ‘yata na kawo ta gaida hajiya
Anano matso gaida asabe itama aiki takeyi anan ‘din.
Cikin sanyin murya tace,
Ina wuni.
Lafiya qlau ya Kika baro mutan gida?
Lafiya qlau”'”tace atakaice.
Saukowar mum asee ne daga sama yasa gwaggo fitowa ananon na biyeda ita kamar jela suka zauna qasan kafet gwaggo na sake gaisawa da mum asee ‘din itama Anano murya na rawa ta gaidata Sai alokacin mum asee ta lura da ita ta tsaida kallonta akanta tsawon mintina ka’dan kafin ta ‘dauke Kai zuwa kallon tv tace,
Gwaggo hinde wacece wannan Kuma?
Hajiya ‘yatace tazo daga qauye sbd wata Yar matsala data samu acan shine nakeson koza’a Kira abdulshakur a sanar Masa zankoma gida.
Qaramin tsaki mum asee taja batareda tasake juyowa gurinsuba tace,
Basai ankirasaba sbd ba da’dewa zaiyi yadawoba kuje idan yadawo kinyi magana dashi koba komai Ina neman sabuwar Mai aikin dazata riqa kularmin da tsaftar Nan sbd asabe ayuka sun fara Mata yawa batamin yanda nakeso.
Hawayen takaici ne suka taru a idanun anano Jin Wai zatai aikatau agidan.
Gwaggo ma jiki asanyaye tace,
To shikenan hajiya Bari muje ta’dan huta taci abinci zuwa gobe tafara aikin.
Bata kallosuba bare ta amsa taci gaba da abinda takeyi na qoqarin canza tashar DStv.
Jiki ba qwari suka miqe suka koma dakin gwaggo
Daqyar tasa ananon taci abinci tayi sallah tasakeyin wanka gwaggoma tasauke abdulshakur tayi Masa Anano. Tabasa madararsa dasukazo da ita ta fulani.
Washe gari tunda safe mum Asee ta Aiko aka Kira Mata ananon jiki asanyaye ta tafi
A dining ta tarar da ita batareda zaune tareda wata kyakkyawar budurwa black beauty tana waya,
Batareda takalli gefenda ananon take ba tace,
Asabe ki nuna Mata ayyukan dazata Kama Miki dasu Kuma ki tabbatarda kin koya Mata Dan kartamin 6anna dankifi kowa sanin bana ‘daukar qaddara.
Tunda asabe tafara nuna Mata ayyukan dazata yi taji hankalinta yayi mummunan tashi Dan ita Koda take qauye Yar gatace Bata Saba da wahalaba Amma data tuno Dan abdulshakur dinta zatai saita fara qoqarin farawa.
Ahankali take aikin cikin nutsuwa sbd gudun banna kotai ba daidaiba.
Tana cikin mopping palon Kamal yashigo yana waya ransa kamar a 6ace ba zato yaji sul6in ruwan data cika gurin mopping din ya jasa saura qiris ya Fadi yakurah data kawo gurin tai saurin taresa tana cewa,
Hey careful.
Ajiyar zuciya ya sauke tareda juyowa ya qurawa fuskanta da tuni tayi wani iri sbd fargaba murya a sanyaye tace,
Yi hkr bansan ya zanyi bane ruwan ya bushe da wuri.
Danne tsananin 6acin ransa yayi sbd qudirin daya qulla akanta tun jiya daya fara ‘dora idanuwansa akanta yasaki murmushi yace,
Ba komai kawai dai ki kiyaye gaba Kuma ki Kira asabe ta qara Miki qarfin AC sbd ya bushe da wuri.
Kallonsa yakurah tayi dakyau cikin mamaki sbd tsaf tasan Kamal Dan iskane na qarshe matuqar baida wata manufa akan wannan yarinyar bazai sakar Mata wannan murmushin ba.
Anano kuwa suna wucewa tabi bayansa da kallo cikin mamakin sanyin halinsa.
Sai guraren azahar tabaro sashen tana shigowa ta fa’da toilet din gwaggo tayi wanka daidai Nan abdulshakur dake kwance a katifa ya tashi daga bacci tayi sauri ta shirya ta dauko madararsa tabasa tasake yi Masa wanka duk da dai ba Sosai ta iyaba.
Wasa ta ringa Mai duk da dai jaririne baisan tanayiba saidai ya bu’de idanu kawai.
Sannu ahankali tafara sabawa da aikin gidan duk da iko da duk wani Shan qamshin mum asee tuni tafara sabawa dashi hakama yakurah Sam ba ruwanta da ita saidai idan zata sakata aiki takira shima tana gamawa take tafiyarta sbd ko kallon arziki Bata Mata.,
Ta 6angaren girki ma itada asabe ne sukeyi yanxu sbd tanason iya ayyuka da dama sbd agida can qauye ko shara batayi bare ta iya wani aiki,
Sunyi sabo da asabe sosai duk da ta girmeta Amma tanajin da’din fira da ita musamman idan tana koya Mata aiki tana Bata labarin kyawawan halayen matar gidan data rasu.
Gwaggo kuwa sosai ta maida hankali gurin taimakawa ananon gurin kulada abdulshakur sbd ganin ba laifi ta saki jiki tana ‘dan Jin da’din aikin datakeyi duk da dai tuni abdulshakur din yadara wayo yafara gane itace uwarsa Dan kusan tsawon wata hudu kenan da zuwanta gidan Kuma har lokacin saheeb baidawo ba Yana Lagos ayyuka sun Masa Dan yawa Kuma dama bason dawowar yakeba.
Ta 6angaren Kamal kuwa tuni wani irin sabo yafara shiga tsakaninsu Dan kuwa wata irin kulawa da mutumta yakeyi ga hidimar siyayyar Kaya dayake Mata kusan duk yafita.,
Hakanne yasa ahankali batareda ankareba soyayyarsa Mai tsanani tashige zuciyarta Wanda tuni yagano hakan Dan dama hakan shine burinsa.
Yau bayan tagamo aikin girkin Rana tashigo ‘dakinsu ta tube tayo wanka tana cikin saka Kaya Mai gadi yazo ya sanarda gwaggo zuwan jafar da baffa Aida sauri tagama sako kayan tasa hijabi tafito itada kanta taje gate tashigo dasu jikinta har rawa yake sbd tsananin farin cikin ganin baffanta da hammanta jafar.
Baffa kasa rufe baki yayi sbd tsananin farin cikin ganin yanda ananonsa ta canxa hankalinta ya kwanta ga abdulshakur shima yayi wani irin girma gashi farine sosai shima Wanda hakan zaisa kace ‘dantane.
Sunci abinci sunyi fira sosai kafin suka miqe suka fita sukayo sallar la’asar a masallacin gidan suka fara Shirin komawa gida.
Har titi Anano ta rakasu jafar na riqeda abdulshakur Yana Masa wasa Sai dariya yakeyi kamar dama can yasansa.
A gabansu motar Kamal ta tsaya ya sauke glass Yana kallonta tasaki murmushi tareda yin qasa dakai tace,
Su baffanane sukazo.
Saurin fitowa yayi ya gaida baffa harda ‘yar rusunawa kafin ya miqawa jafar hannu suka gaisa Sai alokacin idanuwansa suka sauka kan abdulshakur dake hannun jafar yaji gabansa yayi mummunan fa’duwa sbd hakanan saiyaga kamar idanuwansa na nuna Masa kamar yaron da kusan mutum uku na farko kamar nafeesat sbd Dan qaramin bakinsa da fa’din fuskarsa,
Saiyaga kamar Kuma saheeb sbd dogon hancinsa da manyan idanuwansa masu maiqo aciki Sai kuma Anano da kalar fatarsu take iri daya har yellow yellon.
Fa’duwa gabanta ya’dan yi sbd ganin yanda yake kallon abdulshakur Dan haryau ba Wanda ya
san da akwai ‘da agidan.
Cikin sakewar fuska yace,
Muje na sauke ku Tasha Mana.
Aa baffa yace Yana tsayarda Mai adaidaita dayaxo wucewa.
Shiga sukayi jafar ya miqo Mata Abdul suka wuce.
Kallon kallo suka shigayi tsakaninta dashi ya daure yace,
Yaron waye….
Sunkuyar dakai tayi cikin sanyin murya tace,
Dashi nazo.
Wat”””yafada Yana kallon yaron yace,
Yaron nanfa na hannunki nake magana..
‘daga Masa Kai tayi tace,
Eh dashi nazo dama tunfarko.
Shiru yayi baisake cewa komaiba ya wuce yashiga motarsa ya nufi gida.
Itama wucewa tayi na nufi gidan jiki a sanyaye.
Washe gari da safe suna cikin breakfast ya dago ya Kalli mum asee yace,
Mum Anano nada ‘da Wanda ta Haifa..
Ruwan tea ta kurba tareda Kai plantain bakinta tace,
Toni meye hadina da wannan zancen.
Yakurah tace,
Dama tun farko Mai kake tunanin zaisa atattarota akawo wani gurin idanba samun shegeba.
Cikin ‘danjin haushi yace,
Ba haka nasoba Amma ko ahakan ba matsala Zan canxa tsari.
Tundaga lokacin ya canxa tsari ta hanyar nuna tsananin kulawa da qaunarsa ga abdulshakur Dan kuwa har Kaya yake siyo Masa Nan take kuwa yaqara samun kyakkyawan mazauni a zuciyarta ta yanda takejin zata iyayi Masa komai matuqar bai kaucewa addiniba.
Yau tana fitowa da safe Dan zuwa aikinta taga sojoji kusan guda biyar a harabar gidan da Kuma sabbin motoci guda biyu.
Yawu ta ha’diye da cikin fa’duwar gaba tareda dauke Kai Dan itadai tana matuqar tsoron soja
Da sauri ta qarasa ta shige palon tareda sauke ajiyar zuciya.
Kicin ta nufa ta ha’da breakfast sbd yau asabe ce zatai shara da mopping.
Tana gama hada komai ta jera a dining mum asee ce tafito cikin sanyin jiki fuska duk a kumbure ga idanuwanta dasukai wani laushi sbd rashin bacci data Hana kantayi sbd mugun nufinta.
Kallon Anano tayi da qyar tana Zama a kujerar palon tace,
Bani black coffee Mai zafi yanxu.
To tace tareda komawa kicin din.
Cikin nutsuwa da wani irin kwarjinin ya shigo palon Kamal na biyedashi Yana Masa bayanin rashin lafiyar mum asee da rashin cin abinci datake na damuwar rasuwar da haryanxu takasa cirewa aranta.
Wandon uniform dinsa ne ajikinsa Sai farar shirt shade na warby parker da wristwatch na yazole,
Nan take qamshinsa turarensa na signature da clinic for men spray yacika palon.
Kamshin nashiga hancin mum asee ta lumshe idanu wani irin duhu da mugun tirir na shiga zuciyarta sbd tsanarsa da baqin cikin ganinsa.
Gurinta ya nufo direct sbd sauri yake zashi wani taro Kuma shine wakiltacce dazai wakilci soldiers Kuma shine babban baqo.
Tana gama hado coffee din ta zubo a cup ta fito..
Batareda ta luraba ta Dora qafarta inda asabe ta mopping Nan take santsin sauran ruwan mopping din dabai busheba ya jata kafin tayi wani yunkurin tuni cup din yayi sama Sai akan farar shirt dinsa.
Ba Kamal da asabe ba kawai ko mum asee saidata miqe tsaye cikin tsinkewar zuciya.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button