Yadda Tsoron Allah Yasa Shugabam JAMB Ya Maidawa Gwamnatin Tarayya Naira Biliyan 5 !!!
DAGA HAUSA TIMES: Ana cigaba da yabawa fitaccen masanin harkokin addinin nan, Farfesa Is’haq Olanrewaju Oloyede wanda shine ke rike da mukamin rajistara na JAMB bisa maida Naira Biliyan N5 cikin baitul malin Gwamnati.
Rahotanni sunce tun shekarar 1999 ba’a taba samun shugaban hukumar JAMB da ya taba saka ko kwatan kwacin wadannan kudaden ba.
Ana dai ganin galibin wadanda ake dorawa wajen suna amfani da damar ne wajen gina kawunansu amma sai ga musulmi ya bada mamaki cewar wani farfesa
Farfesa Is’haq Olanrewaju Oloyed |
Hausa times ta ruwaito shugaban hukumar zana jarabawar JAMB din ya tara kudaden ne a hawansa mukamin cikin kasa da shekara guda wato a jarabawar 2017.
Bincike ya nuna yanzu haka mista Ishaq yana kokarin ganin ya rage kudaden da ake biya yayin zana jarabawar domin tausayawa masu karamin karfi
Hausa times ta samu bayanin mafi yawanci wadanda ake nadawa a mukamin shugabancin hukumar ta JAMB suna kara komawa wajen Gwamnati ta kara masu kudi domin a cewarsu kudaden basa kai masu.
Da ace shugaban kasa Muhammadu Buhari zai rika samun irinsu farfesa Ishaq to ba shakka da anji dadi cewar mista Olusu
“Indai wannan shi ake kira da musuluntar da Nigeria to ayita nada irinsu Ishaq duk su musuluntar damu” inji shi
Farfesa Ishaq dai babban masanin fiqhu ne kuma kafin nadashi shugabancin JAMB ya rike shugabancin jami’ar Ilorin
Me zaku ce?
Ai ba gwaninta ya yi ba. Domin kudin 'ya'yan talakawa ne da suka zalunta domin su dadadawa gwamnati.