Uncategorized

IZNAH PART 4 : Labari cike Da Makirci

IZNAH Part  4

Hannu ya miqawa ‘daya daga cikin yaransa aka miqo Masa bindiga.
Ciro wata shar6ebiyar wuqa mai Kama da maciji yayi daga takarminsa tareda kallonta cikin rashin imani da rashin tausayi ya damqo wuyanta ya shage da qarfi yace,
Zaki fa’da Mana inda takardun suke ko kuwa haryanzu kinfi buqatar mu aikaki zuwa inda uwar saheeb dinta?
Qoqarin jawo numfashinta dake shi’dewa take sbd shaqar ta rintse ido cikin azaba tafara Shure Shure tana qaqarin 6an6are hannunsa daga wuyan nata.
Cikin takaici yayi wurgi da ita ta fa’di tareda sakin Wani wahalallen nishi Nan take jini ya 6alle Mata ta ‘dago daqyar ta bu’de baki tace,
Dan Allah kayi gaggawar kasheni….
Bata qarasa ba ya saitata da bindiga tareda take cikinta ahasale
Fitsari ne yakusa qwacewa Anano cikin tsananin tsoro da tausayi yasata sakin qara da qarfi Dan tuni tagama jiqewa da zufa da hawaye jikinta ba inda baya rawar tashin hankalin abinda take gani.
A rikice dukkaninsu suka waiga cikin tsananin tashin hankalo Jin qarar alamar ana ganinsu kenan.
Turesa tayi da qarfi tareda tattaro qarfi ta tashi takuma guduwa quryar dajin cikin azaba Dan tuni ciwon mara yafara cin qarfinta
A rikice yace yaransa subita shikuma ya nufi gurinda yajiyo ihun cikin zafin nama Yana gyarawa wuqar hannunsa Zama Dan Koma waye farke cikinsa zaiyi bayan ya qwaqwale idanuwansa daya gansu.
Tana ganin ya nufo gurinta hankalinta yayi mummunan tashi Nan take taji numfashinta na neman barin jikinta sbd tsoro a gigice ta miqe tareda kusawa itama dajin da gudu tana waiwayensa shima tuni ya dafe Mata.
Wata qatuwar bishiya tagani batareda tsoron me zata tarar acikiba tashige cikinta tareda Jan haki ta rufe jikinta tana ‘dauke numfashinta tareda toshe bakinta sbd kukan dake qoqarin fito mata.
Sosai ciwo yafara cin qarfinta ta ‘dafe mararta tana waiwayensu cikin azaba.
Jitayi an fixgota da qarfi a tsorace ta bu’de baki Anano tayi saurin rufe Mata baki tareda sake janyo haki ta rufesu.
Rintse idanuwa nafeesat tayi tareda sakin Wani azababben kuka tana toshe baki sbd azabar datake tsananin ji cikin mararta musamman yanda takeji ruwa nabin qafafunta.
Cikin tsananin kuka da tausayi Anano ta riqe hannunta sbd ganin mummunan halinda take ciki Amma ba halin wani motsi.
Ganin kamar nafeesar zata iya rasa ranta sbd yanda tafara mimmiqewa tana wata irin jijjiga yasa ta leqo kanta bataji motsinsu ba ta fito tareda kamo nafeesar suka fara gudu duk da nafeesar Bata iyawa sosai.
Gasu can ku kamosu su duka akashesu.
Waigawa tayi cikin tashin hankali kafin ta sake matse hannun nafeesat suka fara gudu.
Binsu sukeyi ganin kamar zasuyi musu Nisa yasa ya tsaya tareda saita bindiga ya harba musu.
Wani irin Nishi nafeesa tasaki sbd shigarta da bullet yayi ta fadi kife kan cikinta.
Kuka Anano tasaki cikin tashin hankalin dabata taba ganiba a rayuwarta ta sake kamo hannun nafeesar tanason tada ita.
Girgixa Mata Kai tayi cikin kukan azaba daqyar tace,
Ki tafi,kici gabada gudu karsu kamaki zasu kasheki kema.
Girgixa Kai Anano tayi cikin tsananin kuka tace,
Bazan iya tafiyaba.
Sake kamata tayi suna miqewa tsaye yasake harbowa still nafeesa yasamu tayi baya zata zube Anano tayi saurin riqo hannunta suka zube tare cikin rashin sa’a Ashe sun kawo kusada wani dogon cliff mai tsananin zurfi nan suka fara gangarawa suka fa’da.
Wani qaton dutsi kanta ya daka tasaki nishin azaba Mai qarfi Amma cikin dauriya ta daddafa ta tashi zaune ko gani sosai batayi ga wani irin juyawa da kanta keyi.
Daqyar ta lalabo nafeesa cikin azaba ta juyo da ita daqyar sbd a kife ta fa’do ko motsawa batayiba.
Jijjigata tayi cikin tsananin tsoro da tashin hankali.
Wani irin mugun Nishi taji nafeesar tayi Wanda yayi matuqar Bata tsoro Sai kawai taji Abu a gabanta.
Baya tayi a tsorace jikinta na makyarkyata zuciyarta na bugawa kamar zata bar jikinta.
Cikin qarfin hali nafeesa da numfashi ke qoqarin barin qirjinta ta kamo hannunta ta saka Mata wani irin zobe tareda damqe hannunta cikin azababbiyar murya da Bata fita tace,
Dan allah mena Haifa?
Cikeda tsoro jiki na kyarma ta matso takai hannu na rawa ta tabo murya na rawa tace,
Namiji.
Wani wahallalen Nishi nafeesa tasaki tareda sake damqe hannun Anano murya a karye tace,
Dan Allah ga amana Nan Allah yabaki sbd zuwanki Nan ya nuna kina cikin wannan qaddarar kema,
Nice na haifesa Amma kece Zaki Zama uwarsa sbd wannan itace qaddararmu.
Cikin tsananin kuka da tsoro murya a shaqe Anano tace,
Dan Allah ki daina magana kina bani tsoro..
Wasu hawaye ne suka gangaro gefen idon nafeesar murya na karyewa tace,
Nabaki shi halak malak matuqar Zaki iya riqesa sbd koya koma gidan mahaifinsa kashesa za’ayi kamar yanda aka kasheni hakama za’a kashe mahaifinsa…
Sunan mahaifinsa ABDUL SHAKUR Amma ana kiransa da SAHEEB AB….. Bata qarasaba jini ya 6alle Mata daga mahaifarta Ba qaqqautawa,
Kuka Anano tasaki Mai qarfi lokacinda taga numfashinta ya fita Koda Bata San komai akan mutuwaba ta tababbatarda mutuwace tayi Amma qwaqwalwarta takasa yarda da hakan jiki na rawa tafara
Jijjigata da qarfi cikin kuka Mai tsanani tace,
Meyasa Zaki mutu kibarmin ‘danki alhalin bansan ya zanyi dashiba,
Meyasa qaddara ta raboni da abokanaina na taho na tararda wannan mummunar qaddarar.
Kuka takeyi sosai jikinta ba inda baya rawa.
Cikin sanyin jiki takai hannunta dake matuqar rawa ta ‘dauki yaron Sai kawai ta fashe da wani sabon kukan sbd tsananin tausayin kanta da nasa daya shigeta Dan ko kuka baiyiba bare wani motsi sbd azabar dayasha kafin a haifesa tasan Kuma ba lallaine Suma su samu tsira da ransuba daga hannun Yan daban.
Hijabinta ta zare tareda na’desa aciki ta kaisa qirjinta ta rungume ahankali Nan take taji tsananin qaunarsa na shiga jininta.
Cikin kuka tace,
Bansan dalilin dayasa Allah yakawoka rayuwata ba,
Wannan qaddaratace kaman yanda mahaifiyarka ta fa’da,
Na rungumi wannan qaddarar da hannu biyu nayi alqawarin riqeka tamkar Dan dazan Haifa,
Nayi alqawarin Zama jajirtacciyar uwar da bazan Bari Akira da gurbataccen sunaba matuqar ina Raye Kuma nayi alqawarin jure komai zai biyo.,,
Kukantane yafara qara sauti tayi saurin cusa Kai cikin qafafuwanta sbd Kar sujiyo sautin kukan..

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button