Uncategorized

IZNAH PART 3 : Labari Cike Da Makirci

IZNAH PART 3

3:00 pm girls college…..
Zaune take bakin bishiyar da bus ‘dinsu ke Lodi tana rero waqarta cikin farin ciki qarshe tashi tayi tana jujjuyawa tareda qara sautin waqarta,
Hannu tasa ta jawo hannun ubaidah tana cigaba da jujjuyawa.
Nusaiba data nufo gurin da ruwan pure water guda uku a hannunta data siyo musu tayi saurin qarasowa cikin rawa tana bin waqarda dataji Anano tanayi cikin farin ciki.
Kallonsu ubaidah tayi bayan ta Sha Rabin ledar ruwa ‘daya tasaki qaramin tsaki tana girgixa Kai kafin tace,
Wai Dan Allah Anano ku yaushe zaku San kun fara girma,
Ko kunya bakwaji dai yanxu gaban mutane da dama kuke rawa Kuna waqa.
Wani juyi tayi tareda kar6ar ruwa ‘daya ta bu’de ta ‘dansha kafin tazauna kusada ubaidah ‘din fuskarta ta canxa zuwa yanayi sanyi ahankali tace,
Inason ne nayi duk wani farin ciki a yau kafin nakoma gida sbd hakanan zuciyata ke Jin kamar yau itace ranar farin cikina wata qila na qarshe ko Kuma mabudin wani sabon farin cikin.,,
Kallon nusaiba tayi jikinta na tsananta sanyi tace,
Nusy kece kusan komai na halayyarmu yake ‘daya kinajin yanda nakeji ayau kuwa?
Kallonta nusaiban tayi tareda kamo hannunta tace,
Anano banajin komai a zuciyata Sai tsantsan farin ciki dason ganin na Isa gida da wurwuri.
Kafin suyi wata maganar direba yace kowa ya shiga mota angama shirya Kaya.
Miqewa suka tareda sake bankwana da sauran abokanansu cikin kewar juna dazasuyi suka shirshiga motar.
Acan baya suka zauna Anano ce bakin window Sai nusaiba a gefenta kafin ubaidah da wata ‘yar qauyensu Nana.
Cike bus ‘din take taf da ‘dalibai ‘yan qauyensu da wa’inda qauyensu yake gaban nasu maza da Mata.
Tunda suka ‘dau hanya taji gabanta na tsananta fa’duwa Nan take mararta ta fara mur’dawa ta lumshe ido tanajin lokacinda period yazo Mata gashi idan tana period sosai take rushing.
Kallon nusaiba tayi cikin sanyin murya tace,
Wlh jinake kamar na rufe Ido naganni cikin gida musamman yanxu Da jini yazo Mata tasan kafin akai koyayane saitayi staining.
Qaramin tsaki taja lokacinda taga har magriba tayi musu ahanya sbd yanda drivern ke tuqi sbd tsufa da rashin isashiyar lafiyar motar Dan sun tsaya gyara yafi so uku a hanya gashi still da akwai sauran tafiya.
Qarfe tara da minti arba’in motar ta qara tsaya musu a hanya wannan karon suna kusa da shiga qauyen nasu ne,
Duk Wanda ke motar ba Wanda yake cikin walwala sbd tuni suka gaji da Zama da Kuma tafiyar kowa a matse yake daya Isa gida sbd ga yunwa ga qishirwa ga dare dayayi musu Dan tuni sawu suka fara ‘daukewa.
Firfitowa sukayi kowa na sakin tsaki dattijon direban kuwa bu’de gaban motar yayi ya fara ‘dan duddubawa gwanin tausayi sbd shima yau ‘din motar tafi basa wahala.
Ita ka’daice Bata fitoba sbd sanin datayi kayanta sun Jima da lalacewa.
Wani tunani yashigeta lokacinta wata tsohuwar a Kori kura ta wuce ta haska hanyar dasuke…
Murmushi tasaki cikin farin ciki tareda tasowa ta fito motar tana sake kallon hanya.
Juyawa tayi cikin murna zata kirasu ubaidah saitaga duk sun tsallaka titi gurin yin fitsari Sai kawai ta juyawa tareda cewa,
Kusameni a gida Dan nasan saina rigaku idan nabi ta gonar Nan.
Gangarawa tayi batareda tsoron komaiba sbd idanuwanta sun rufe dason ganin ta Isa gida Dan murna da farin ciki.
Saidata kutsa sosai cikin dajin taja cak ta tsaya sbd motsin mutane da kunnuwanta suka jiyo mata.
Fa’duwa gabanta yayi Amma saita cigaba da tafiyarta
Sake Jin wani babban motsin tayi sai tasake saurarawa taji ba tantama motsine Kuma kamar kusanto gurin datake motsin yake.
Jujjuyawa tayi gabanta nadan faduwa cikin tsananin tsoro da fargaba bataganin komai sbd duhun dare hasken farin watama datayi tunanin zai hanatajin tsoro harta Isa gida tsawon shukar masara da gero duk ya hanata ganin hasken.
Sake juyawa tayi da qarfi Jin sawun gudu na kusanto inda take nan take hankalinta yafara tashi tafara qoqarin juyawa tana kutsawa cikin shukar batareda tasan inda take saka qafartaba.
Ji tayi wata qatuwar muryar data qarasa hargitsa kayan cikinta tana cewa,
Karku Bari ta tsare ku kamo ta kota halin qaqa araye ko amace.
Qara qaimin gudunta tayi tana waiwayen bayanta duk da Bata ganin komai gashi tuni tayi Nisa ma da hanyar garinsu tabi wani 6angaren dayayi nesa sosai da garinsu batareda tasaniba.
Tsayawa tayi jikinta na tsananin rawa tafara waige waige sbd Jin sun kusa isowa daf da ita.
Kukane ya qwace Mata ta nufi wata qatuwar bishiya ta lafe cikin hakukuwan qarqashinta jikinta na tsananta rawa ta rintse idanuwanta.
Ahhhh…taji wata tattausar muryar mace ta fa’da cikin azaba da yanayi na wahala.
Bu’de idanuwanta tayi da sauri jikinta na same karbar rawa,,
Mace tagani da tsohon ciki ta fa’di kife kan cikin tafara qoqarin tashi cikin aza6a sbd tacigaba da gudu.
Qoqarin tashi take suka iso tareda zagayeta su biyar kowannensu fuska ba ‘digo ko alamar imani sbd daka gansu kaga makasa mutane ta kowace irin hanya.
Dafe cikinta tayi da hannu ‘daya cikin tsananin azaba da hawaye tafara qoqarin tashi babban cikinsu ya ‘daga hannu ya kwasheta da wani irin gigitaccen mari saidata sake kifewa kan cikinta tasaki wata azababbiyar qara Mara sauti sosai sbd qarfinta daya fara qarewa.
Qafa yasa ya mirgina ta tareda taka cikin da qarfi yace,
Ko kafa’da Mana inda kika 6oye takardun Nan ko na harbe cikin jikinki ayanzu.
‘dago fuskarta tayi cikin tsananin azaba tana hawaye tace,
Har abada bazan fa’di inda takardun sukeba,
Na gwammace na mutu akan na fa’di inda takardun suke Dan kawai a tarwatsa rayuwar SAHEEB.
wani mugun duka yakaiwa bakinta tareda sake take cikinta cikin 6acin Rai dai zuciyarsa takai maqura gurin qonuwa Dan shi baya tsayawa dogon zance yake aika mutum lahira Amma wannan tun safe dasuka satota take wahalardasu .
Waya ya fitar Rai a6ace ya Danna Kiran mum.
Rai a 6ace itama ta ‘daga sbd Sam takasa samun nutsuwa Sai nafeesat tafadi inda takardun kadarorin saheeb inda suke.
A hasale cikin muryar cikakken ‘dan ta’adda yace,
Hajiya wannan fa taqi fa’da gashi tana neman 6ata Mana aiki Dan yanzu hakama so biyu tana guduwa mun kamata yanxu hakama muna dajin wani qauye da ita acan nesa.
Miqewa tsaye tayi daga kan kujerar datake cikin rashin imani da takaici tace,
Bullet ku sake tambayarta for the last time idan taqi fa’da ka saita bindiga a cikinta ka harbeta idan Bata mutuba ka qara Mata ‘daya saiti da zuciyarta.
‘dif ta kashe wayar tana gama fa’da tareda kallon ‘danta dake zaune Yana kallonta shima Rai a6ace tace,
_KAMAL_ ka Kira saheeb ka sanardashi matarsa ta gudu tun asuba ba’a gantaba,
Idan ya tambayeni kace Masa hawan jinina ya tashi Sarah taban magani Nasha nayi bacci.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA