Addu’a A Asirce (1) Dr Muhammad Sani Umar R/Lemo
Ramadaaniyyat-Kashi Na Biyu – 2
Dr. Muhd Sani Umar
Addu’a A Asirce (1)
1. Allah (S.W.T) ya yabi Annabi Zakariyya (A.S) da cewa, ya roƙi Allah a asirce, yana mai cewa, (Lokacin da ya kira Ubangijinsa ya roƙe shi a asirce). Wannan ya nuna mahimmancin yin addu’a a asirce.
2. Yin Adda’a a asirce ita ce al’adar magabata na ƙwarai cikin wannan al’umma, Alhasan Al-Basri yana cewa, “Musulmai sun kasance masu matuƙar ƙoƙarin roƙon Allah, amma ba a jin su suna daga muryoyinsu wajen addu’a, suna yin ta ne da murya ƙasa-ƙasa, saboda Allah yana cewa, (Ku roƙi Ubangijinku cikin ƙasƙantar da kai da sussauta murya). [Al-A’raf, aya ta55”].[Ibnul Mubarak, Azzuhud, #140].
3. Allah ya yi umarni da a roƙe shi da murya ƙasa-ƙasa, kamar yadda ya gabata, domin yin haka ya fi nuna ikhalasin bawa da ƙasƙantar da kansa ga Allah.
4. Don haka yin gangamin addu’a abu ne da ba shi da madoga a cikin aikin magabata, in ban da a cikin ibadu da aka san ana yin su ne cikin jama’a, kamar addu’ar shayar da ruwa ko kusufin Rana da Wata, ko addu’ar alƙunut ko addu’ar liman a kan minbarin juma’a da makamantansu wadanda nassi ya zo da su.
Sources:darulfatawa.com