Uncategorized

IZNAH Part 2 : Labari Cike Da Makirci

IZNAH PART 2

 yake  Kwance bakin swimming pool sanye da 3quater kawai cikin Yar qaramar rumfar shaqatawa dake gurin idanuwansa a lumshe kamar Mai bacci Amma ba baccin yakeba farar fatarsa Sai wani kyallin hutu da kyau take musamman dayake ba Riga ajikinsa.
Bu’de fararen oily eyes ‘dinsa yayi ahankali tareda Kai hannu kan table ya’dau wayarsa akaro na ba adadi ya sake Danna kiranta.
Switch off yakumaji ya tashi zaune zuciyarsa ba da’di sbd wannan karon shine karo na farko daya ta6a Kiran nafeesat tun bayan aurensu Amma wayarta akashe.,
Miqewa tsaye yayi tareda sake Danna kiranta still akashe.
Kasa daina Kiran yayi Saida yajera Kiran kusan so ashirin Amma baya samu,,,
Hannuwansa ya zura a aljihun wandonsa tareda tsayawa bakin swimming pool’din ya qurawa ruwan Ido cikin tunani.
Tunda ya auri nafeesat tsawon shekara biyu kenan Amma bai ta6a ‘daga waya yakirataba sbd kullum itace Mai kiransa safe Rana dare harsai ya gaji ya kashe wayoyinsa sbd yanda yake damuwa da kiranta.
Sam Bata fushi da yanda baya kiranta itadai burinta takirasa taji ya yake,
Idan kuwa Yaje Yana tareda ita to batada Zama ta dingi hidimarsa Dan taga ta kyautata Masa ko Kuma taga murmushinsa ko sau ‘daya ne Amma bai ta6a ba.,
Nafeesat nada haquri da juriyarda ba kowace mace ce keda itaba,
Wani irin so Mai qarfi na haqiqa take Masa Wanda tun farko yasa ya amince ya aureta sbd ta sadaukarda duk wani farin cikinta akan soyayyarsa,
Bayan aurensu Bata tsinci komai ba Sai baqin ciki da rashin kula tareda halin ko inkula dayake nuna Mata Wanda tsill ta danne sbd Bata ganin laifinsa ko ka’dan,
Tun kafin ta auresa harta auresa Bata ta6a ganin dariyarsaba kosau ‘daya duk iya qoqarinta na ganin hakan bata samuba sbd Babu so ko farin ciki dayakeji a rayuwarsa ko ka’dan,
Iya qunci zuciyarta na quntatuwa da yanda ta fahimci ba soyayyarta ko ‘digo a zuciyarsa,
Tayi kuka a 6oye tayi a bayyane Amma takasa samun matsuguni a zuciyarsa duk da Yana soja Sam bayada zafin Rai kamar na sauran soldiers shiyasa take qara tsananin sonsa sbd he’s calm.
Hakanan ta haqura ta fawwalawa Allah komai tacigaba da kyautata Masa Wanda sannu ahankali tsananin tausayinta ya shigesa sbd hkr da tsananin qaunar datake Masa har Bata ganin laifi ko kuskuren duk abubuwan dayake Mata musamman yanda ko Zama bai cikayi a qasarba.
Dawo da ita LA yayi gurinsa tareda tursasa zuciyarsa Bata kulawa,
Gwargwado yanayin iya qowarinsa gurin Bata kulawa da soyayya Wadda ita azahirin gskia tasan yanayi ne Dan ya faranta ranta,
Cikin ikon Allah ahaka har ciki ya bayyana ajikinta,
Bata ta6a tunanin arayuwarta zatagansa cikin farin cikiba Saida yaji maganar cikin Wanda tun daga time ‘din ya qara ninka kulawarsa akanta sbd ayanxu Babu abinda yakeso sama da abinda ke cikinta sbd yanda rayuwarsa ke cikin quncin rashin uwa,uba ko wani ‘dan uwa dazai kalla yaji farin ciki Sai yanxu dazai samu ‘dan kansa jininsa shiyasa ahankali sonta da tausayinta suka fara samun kyakkyawan guri a zuciyarsa.
Tunda ta auresa ta gano qunci da ka’daicin da zuciyarsa take ciki ta maida dukkanin adduarta akan Allah yakawo farin ciki Mai ‘dorewa cikin rayuwarsa musamman data gano mum asee da qaninsa ba qaunarsa sukeba dukiyarsa suke Hari.
Koda cikinta yafara tsufa ya maidata gida Nigeria sbd ta haihu acan bayan ya saka an ‘dauko dattijuwar dazata kula da ita duk da su mum na gidan.
Kullum itake kiransa tun asuba har dare Bata gajiya da Kira Koda bai ‘daukaba saitabar Masa voice note Amma yau akaro na farko da gari ya waye har Rana ta fa’di Bata kirasaba Wanda yasan tabbas Dole akwai mummnan dalilin daya Hana Dan Bata yarda takasa kiransa komai rintsi.
Sake lumshe fararen idanuwansa yayi tareda qara ‘daga wayar ya sake danna kiranta.
Same thing yakuma ji switch off,.
Agogon hannunsa ya kalla yaga time yasan yanzu Nigeria suna gaf da Kiran magrib.
Wayar mum ya latsa Kira tayita ringing ba’a ‘daga ba
Ya sake Kira kusan four Misscalls ba answer.
Ji yayi hankalinsa ya fara mummunan tashi Dan hakanan yakejin nafeesan batada lapiya,
Rintse idanuwansa dasuka fara canxa launi yayi yanajin son ganinta dason ganin lafiyarta data babynsa na shigarsa ya bu’de idanuwa ya Danna Kiran wata number.
Ringing biyu tayi aka ‘daga daqyar ya bu’de baki cikin wata irin lallausan classy voice yace,
Koma me kakeyi kayishi cikin Daren Nan kaje kayi Mana booking we’re going home to tomorrow.
Wat? Are you kidding me?……
Datse wayar yayi Yana yamutsa fuska sbd bazai iya tsayawa sauraron sauran zancen zayyan ‘dinba sbd zai iya sakar Masa wani headache ‘din bayan Wanda yake fama dashi yanxu.

Mu hadu kashe na ukku.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button