Dole Sai Muna Kai Hare-Hare A Wasanninmu Na Gida -Pogba
Dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Paul Pogba, ya bayyana cewa dole sai kungiyar ta dage tana yawan kai hari musamman idan tana buga wasa a gida idan har suna son sukai ga gaci.
Pogba ya bayyana hakane bayan kungiyar ta tashi daga wasa 1-1 da kungiyar kwallon kafa ta Wolverhampton a wasan sati na biyar na gasar firimiya da a yanzu ake bugawa.
Manchester United dai tasamu maki daya ne kacal cikin wasanni biyu data buga a filin wasanta sai dai kuma ta samu nasarar wasanni uku data buga a waje akan kungiyoyin Burnley da Watford da kuma kungiyar Young Boys a gasar zakarun turai
“Idan muna buga wasa kawai babu abinda za mu dinga tunani sai dai kai hare-hare saboda bamu da inda yafi gidanmu kuma munfi samun dama a gida kamar kowacce kungiya saboda haka akwai bukatar sake lissafi” in ji Pogba
Ya ci gaba da cewa “kungiyoyi suna jin tsoronsu idan suna buga wasa a gida saboda haka dole sai suna yawan gudu a fili suna kai hari ba sassautawa kamar yadda mukayiwa Liverpool da Chelsea da Tottenham a shekarar data gabata”
A yau ne dai kuma Manchester United za ta buga wasanta na gaba da kungiyar kwallon kafa ta Derby County, wadda tsohon dan wasan Chelsea da Ingila, Frank Lampard yake koyarwa

