Majalisar Zartarwa Ta Amince Da Kashe Naira Bilyan 185 Domin Gyaran Tituna Guda 14 A Fadin Kasar Nan
Adesina, wanda ya yi bayani a madadin ministan ayyuka da gidaje da wutar lantarki, Babatunde Fashola, ya zayyano ayyukan kamar haka:
1. Titin Gwoza – Damboa – Goniri – Ngamdu a jihohin Yobe/Borno wanda kamfanin Hajaig Construction Nigeria Ltd zai yi kan naira bilyna 34.608.
2. Titin Mayo Belwa – Jada – Ganye – Torngo a jihar Adamawa wanda kamfanin Messrs Triacta Nigeria Ltd zai yi kan naira bilyan 22.699.
3. Titin Ado – Ifaki – Otun – Kwara a jihar Ekiti kan naira bilyan 6.002.
4. Gyaran gadar Makurdi a jihar Benue wanda kamfanin Messrs AG Visio Construction Ltd zai yi kan naira bilyan 4.617.
5. Gyaran titin Ihugi – Korinya -Wuse -Ankor a jihar Benue wanda kamfanin Datum Construction Ltd zai yi kan naira bilyan 15.641.
6. Gayran titin Gbagi – Apa – Owode a garin Badagry jihar Lagos wanda kamfanin Messrs Smithcrown Nigeria Ltd zai yi kan naira bilyan 4.366.
7. Gyaran titin Ijebu Igbo – Ita Egba Owonowen a jihohin Ogun da Oyo wanda kamfanin Messrs DC Engineering zai yi kan naira bilyan 9.833.
8. Sabunta titin Jattu – Fugar – Agenebode a yankin Edo Phase II wanda kamfanin Mothercat zai yi kan naira bilyan 7.506.
9. Makurdi – Gboko – Wannune – Yander Section 1 a jihar Benue wanda kamfanin Messrs Rockbridge Construction Ltd zai yi kan naira bilyan 18.669.
10. Gyaran Tsohon titin – Enugu – Poth Harcourt dake yankin Agbogugu a jihar Abia, wanda kamfanin Messrs Setraco Ltd zai yi kan naira bilyan 13.933.
11. Gyaran hanyar Umulungbe – Umoka kan naira bilyan 6.249.
12. Titin Amokwu – Ikedimkpe – Egede – Opeyi Awhum dake jihar Enugu wanda kamfanin Messrs IDC Construction zai yi kan naira bilyan 21.729.
13. Sabunta titin Nkwu Inyi – Akpugoeze a jihar Anambra wanda kamfanin Anbeez Services kan naira bilyan 2.595
14. Gyaran titin Sabon Birnin – Tsululu – Kuya – Maradi Junction a jihar Sokoto wanda kamfanin Messrs China Zhonghao Nigeria Ltd zai yi kan naira bilyan 4.354




