JIBWIS Sheikh Bala Lau ya samu mukami a turai
An nada shi a matsayin shugaban ahlus-sunnah na nahiyar turai baki daya
Shugaban kungiyar Izalatul bidia wa ikamatu-sunnah na Nijeriya Sheikh Bala Lau ya samu sabon mukami na zama shugaban ahlus-sunnah a turai.
Bayan gayatar da babba malamin ya karba daga kungiyar Sautus-sunnah na nahiyar turai kwanan baya an ka nada shi a matsayin shugaban ahlus sunnah na nahiyar kasashen turai baki daya.
“Mun yi nazarin kungiyoyi-kungiyoyi na Musulunci da Ahlus Sunnah a duniya, sama da kungiyoyi sittin (60), a kasashe daban-daban. Amma ba mu ga kungiyar da Allah Ya ba nasara cikin takaitaccen lokaci irin wadda Ya ba kungiyar Izala ba” inji jagoran kungiyar sautus-sunnah na kasar turai.
Bisa ga labarin da jaridar Rariya ta fitar, kungiyar sautus-sunnah ta kara gina ma kungiyar Izala ofishi karkkashin cibiyar ta.
Join Our WhatsApp Channel
Get verified job vacancies, career tips, scholarships and opportunities delivered straight to your phone, free and as soon as they're posted.






