Kannywood

Kano Muhammadu Sanusi ya goyi bayan ‘yan fim

Fina-finai a Najeriya na taka muhimmiyar rawa wajen hada kan ‘yan kasa tare kuma da tabbatar da raya al’adun al’ummar mu inji Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi Lamido na biyu.

Sarkin na Kano dai yayi wannan bayanin ne a yayin da wasu fitattun ‘yan fim din daga masana’antar shirya fim din Hausa na Kannywood da kuma na fina-finan ‘yan kudancin Najeriya watau Nollywood suka kai masa ziyara a fadar sa.

NAIJ.com dai ta samu haka zalika cewa Sarki Sanusi ya kuma bayyana cewar ko shakka babu haduwar jaruman fina-finan daga masana’antun kudu da Arewa da cewar abu ne mai kyau da zai dada kara hadin kan al’ummar kasar musamman ma a yanzu da siyasa ta raba kawunan mutane da dama.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button