Labarai
Da A Ce Zan Musulunta, Da Ni Ma Sai Na Yi Mauludi, Inji Obasanjo
Advertisment
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa da a ce zai musulunta da shi ma zai rika yin bikin Mauludi, a gidansa kuma zai rika yin shagulgula fiye da yadda ake yi a yanzu.
Obasanjo wanda ya bayyana hakan a lokacin da wasu matasan kabilar Yarabawa da Ibo mabiya addinin Musulunci, suka ziyarce shi lokacin da suka kammala gudanar da zagayen Mauludi a kauyen Otta, daga karshe ya sanya wa matasan albarka.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com