Labarai

Saudiya ta ƙaddamar da manhajar neman bizar Hajji da Ummara ta wayar salula

Saudi Arebiya ta ƙaddamar da wata manhaja ta neman bizar Hajji da Ummara ta wayar salula a Birtaniya.
Saudiya ce ƙasa ta farko a duniya da ta ƙirƙiro da hanyar yin rijistar biza ta wayar salula.
Daily Nigerian Hausa ta gano cewa sabuwar manhajar za ta baiwa maniyyaci dama ya shigar da duk bayanansa da hotuna, ya kuma ajiye sau kafin ya je ofishin buga bizar domin karɓo wa.
Sai dai kuma dole ne bayanan da maniyyaci ya bayar a manhajar ya kasance ya yi daidai da wanda zai kai ofishin buga bizar.
An kirkiro da wannan sabuwar hanyar domin saukaka hanyoyin kula da boda a Birtaniya.
Tun a bara ne dai Ministan Harkokin Waje na Saudiya, Faisal bin Farhan ya ƙaddamar da manhajar bisa umarnin Yarima Muhammad Bin Salman.
Manhajar kuma ta samu ne da haɗin gwiwar hukumomi da dama na harkokin Hajji da Ummara a Saudiya.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button