Labarai

Wata cuta mai kama da Ebola ta kashe mutane a Uganda

Advertisment

Wata cuta mai kama da Ebola da masana kiwon lafiya ke kira Marburg, ta yi sanadiyyar mutuwar mutum biyu a Uganda.

Ma’aikatar kiwon lafiyar kasar ta ce bayan gwaje-gwajen da aka gudanar a kan gawarwakin mutanen biyu da suka mutu, an tabbatar da cewa cutar ce wadda ke haddasa tsiyayar jini a cikin jikin dan adam ta yi sanadiyyar ajalinsu.

Cibiyar binciken cututtuka masu yaduwa a kasar, ta ce cutar da ake kira Marburg ta soma bula ne a kasar cikin wani yankin da ake kira Kamwenge a shekara ta 2007.

Cutar da ke yaduwa kamar Ebola, a shekara ta 2012 ta yi sanadi rai 10, kazalika a 2014 ta kashe mutun guda.
Marburg sunan wani yankin ne na Jamus, inda aka fara samun bular cutar a shekara ta 1967.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button