Labarai

Badakalar NNPC: Shehu Sani Ya Nemi Buhari Ya Yi Murabus Daga Ministan Mai

Advertisment

Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani ya kalubalanci Shugaba Muhammad Buhari kan yi ajiye mukamin Babban Ministan mai bayan da karamin Ministar mai, Ibe Kachikwu ya rubuta masa wata wasika inda ya fallasa yadda Shugaban kamfanin mai na kasa ( NNPC), Baru ke yin gaban kansa wajen tafiyar da kamfanin.

Dan majalisar ya nemi Buhari da ya binciki zargin da karamin Ministan ya gabatar a kan shugaban kamfanin NNPC wanda a cewarsa, ta haka ne kadai Buhari zai tsira da mutuncinsa. Tuni dai, majalisar Dattawa ta kafa wani kwamiti wanda zai binciki Shugaban kamfanin na NNPC.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button