Labarai

Sunayen shugabannin ‘yan bindiga 78 dake Arewacin Najeriya da yawan mabiyan su

Sunayen shugabannin ‘yan bindiga 78 dake Arewacin Najeriya da yawan mabiyan suDuka-duka mako biyu kenan, bayan ayyana yan fashin daji da suke addabar arewacin Nageriya a matsayin yan ta’adda, sai kuma ga jerin sunayen barayin da yaransu na jihar Zamfara ya bayyana.
Jaridar Vanguard da labarunhausa ta hada rahoto cewa, wani farfesa a jami’ar Sokoto, Murtala A. Rufa’i, a wani littafin sa mai suna ‘I am a Bandit’ ma’ana (Ni Barawon Daji ne) ya lissafo sunayen shugabannin yan fashin da kuma adadin yaransu.
A fadar Rufa’i, an samo sunayen ne daga kauyuka daban-daban kusa da inda sansanonin yan ta’addan suke.
Karamar hukumar Muradun
1.Sama’ila na Bayan Dutsi yana dayara 150 Jimmo Fadama na Bayan Ruwa yana da yara 80
2.Simoli Jaya na Bayan Ruwa yana da yara 65
3. Sahabi na Bayan Ruwa yana da yara 250
4.Na’akka na Bayan Ruwa yana da yara 180
5. Aminu Jajani na Bayan Ruwa yana da yara 120
6. Sani Ba ruwanka na Dagwarwa yana da yara 135
7. Uban Kafirai na Dagwarwa yana da yara 250
8. Mai bokolo na Dajin ‘Yar Tunniya yana da mabiya 300
9. Haruna Zango na Dammaka yana da mabiya 280
10.Muntari na Duddubi yana da yara 31
11.Ɓoyi na Dudduɗi yana da yara 210
12.Turji na Fakai yana da kimanin mabiya 500
13.Nakyalla na Filinga yana da mabiya 213
14. Najana na Gidan Bisa yana da yara 96
15. Sitanda na Gwari yana da yara 156
16. Dullu na Sububu yana da yara 138
17.Halilu Sububu na Sububu yana da sama da mabiya 1,200
18. Maiduna na Tankyalla yana da mabiya 216
19. Gwaska na Tungar Kolo yana da yara 76
20. Kabiru ‘Yankusa na Safrar Kaɗe yana da yara 185
21. Ƙaramin Gaye na Tungar Miya yana da yara 242
22. Ɗan Sa’adiya na Dagwarwa da Bamako yana da yara 48
23. Ɗan Shehu na Kudo yana da yara140
24.Mati of Kudo yana da yara 165
25. Ɗan Bello na Kudo yana da yara 98 Masarautar Dansadau
26. Ɗan Makaranta na Madaka ta Arewa yana da mabiya 460
27. Dogo Gyaɗe dake Dajin Babar Doka yana da kimanin mabiya 2000
28. Damana a Dajin yana da kimanin mabiya1500
29. Ali Kacalla na Madada yana da kimanin mabiya 1600
30. Malam na Cebi ta yamma yana da kimanin mabiya 900
31. Bulaki na ‘Yargaladima ta gabas yana da kimanin mabiya1200
32. Ciyaman a ‘Yargaladima ta gabas yana da mabiya 900
33. Ɗahe a ‘Yar galadima ta gabas yana da sama da mabiya 250 35. Kawu na gabashin Ɗansadau yana da sama da mabiya 700
34. Ado Lalo na Ɗansadau ta gabas yana da 350
35. Bulak dake Ceɓi ta gabas yana da kimanin yara 520
36. Janburos na of east Madada ta gabas yana da yara 800
37. Sani Bica dake gabashin Madaka yana da kimanin yara 180
38. Ɗan Bagobiri na yammacinof Ceɓi yana da sama da yara 230
39. Nagala dake Mairairai ta yamma yana da 750
40. Ali ƙanen Nagala yana da yara 220
41.Zahiru yana da 175
42. Mai Gariyo dake kudancin Burwaye yana da yara 56
43. Yalo na kusa da Burwaye yana da yara 85 Karamar hukumar Zurmi
44. Kachalla yana da yara 1200
45. Maidaji yana da yara 1500
46. Ɗanƙarami yana da yara 750
47. Karamar hukumar Birnin Magaji
48. Alhaji Zaki yana da yara 85
49. Yalo na Rugu yana da yara 60
50. Hassan na Rugu yana da yara 28
51. Maidaji na Rugu yana da yara 40
52. Kachalla na Rugu yana da yara 58
53. Karamar hukumar Shinkafi
54. Atarwatse na Dajin Mashema yana da yara 200
55. Ɗan Maƙwado na Kamarawa da Bafarawa yana da yara 550
56. Nagona a tsakanin Bafarawa da Surduƙu yana da yara 200 Karamar hukumar Tsafe
57. Idi dake Guga yana da yara 100
58. Baba Yayi a Guga yana da yara 100
59. Juuli na Kwankwanba yana da yara 100
60. Tukur na Munhaye yana da yara 90
61. Alhaji Ado Aleru dake Munhaye yana da kimanin yara 2500
62. Mabi dake Munhaye yana da 100
63. Ɗan’ Ibiro na Munhaye yana da yara100
64. Guntu dake Munhaye yana da yara 65
65. Karki dake Munhaye yana da yara 70
66. Lawali Bunka dake Munhaye yana da yara 80
Shugabannin barayin da basu da takamaiman adadin yara
67. Shehu Bagewaye
68. Dancaki Odita
69. Standard da Sani black
70. Kabiru Maniya
71. Malan Ila
72. Rageb
73. Kacalla Haruna
74. Katare
75. Hasan
76. Husaini Jaja na Gusau
77. Dogo Hamza na Bukkuyum
78. Auta na Anka
Barayin da suka kware wajen aikata manyan laifuka, kama daga fashin daji, garkuwa da mutane, satar shanu, fashi da makami da kashe-kashen mutane, sun dade suna addabar arewacin Nageriya.
A wani rahotonni da suka bayyana a baya, barayin sun rubuta wasiku zuwa ga wasu al’ummu mazauna karamar hukumar Bukkuyum, a jihar Zamfara, cewa ko su biya kudi su tsira da ransu, ko su fuakanci hareharen yan ta’addan.
Yan fashin dajin Gando ne suka rubuta wasikun. An rubuta wasikun ne da Hausa kuma aka aika zuwa garuruwan.
Kowacce wasika tana dauke da sunan garin da aka tura zuwa garesu, a saman wasikar, da kuma kudin da zasu biya. Kuma an rubuta bambar waya da zasu kira.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA