Kannywood

Kanwar Samira Ahmad Ta Fara Fim Da ƙafar Dama

Advertisment

Abdul Amart Maikwashewa ya shirya Gabatar da sabuwar Jaruma acikin fim dinsa mai suna Ranar Aurena, Aseeya Ahmad kanwace ga tsohuwar Jaruma Samira Ahmad wadda itama ta taka mihimmiyar rawa a duniyar kannywood kafin aurenta da angonta TY sha’aban.

Aseeya kyakkyawace sannan masu sharhi akan jaruman kannywood suna Hasashen cewa jarumar zata fara da kafar dama domin Ganin ta bulla a kamfanin “Abnur Entertainment” sun dade suna Gabatar da manyan finafinai, Irinsu Aisha Humairah, Ummi, Ma’aurata, Zeenat, Mijin Biza da kuma Minal, wadannan wasu da cikin manyan finafinai ne wadanda kamfanin suka gabatar.

Abnur ( Ab-dulNur-a) bisa hadin Gwiwar abokan juna Nura M Inuwa da Abdul Amart sun fara daukar fim din a ranar Laraba 16 ga Augusta, wanda zai samu aiki daga Babban Darekta Sadiq N Mafia.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button