Kannywood
Rayuwar Matan Arewa Cike Take Da Kalubale – In Ji Jaruma Rahama Sadau
Daga Habu Dan Sarki
Jarumar Hausa Fim Rahama Sadau ta bayyana cewar, rayuwar yar Arewa mai hankoron zama wani abu nan gaba cike take da cikas iri-iri.
Sadau ta yi wannan batu ne a tattaunawa ta da jaridar Thisday. Jarumar ta ce dakatar da ita da aka yi a harkar fim din Hausa ya janyo ta sake samun wasu sabbin hanyoyi a harkar fim na cikin gida da waje.
Jarumar ta ce a kullum tana kokari wajen kare mutuncinta da kuma al’adarta a lokacin da take harkar sana’ar fim na turanci wanda aka yi a kudancin Nijeriya.
Sadau ta ce ko cikin kwanakin nan ta ki amincewa da yin wani fim na turanci wanda aka bukaci ta fito a matsayin ‘yar madigo.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com