Uncategorized

Buhari nason wargajewar kasar nan kafin 2019- dole ne mu wakilan alumma mudauki mataki, AHMED YERIMA MISAU,

Buhari nason wargajewar kasar nan kafin 2019- dole ne mu wakilan alumma mudauki mataki, AHMED YERIMA MISAU,

Ahmed yerima dan majalisar taraiya daga jahar bauchi mai wakiltar mazabar misau da dambam a majalisar taraiya yace Buhari nason wargaza kasarnan kafin zaben 2019, ya kara dacewa buhari baya bin raayin talakawa sai dai nasa a lokacin kamfen buhari yayi alkawura wa talakawa wanda har yanzu buhari bai cika ko daya ba hasalima har yanzu ko hanyar cika wadannan alkawuran buhari bai dauka ba, munyi wa talakawa alkawarin cewa idan suka zabemu zamu inganta musu rayuwarsu sai gashi kuma ayau talaka na cikin ukuba a yanzu akasarnan, abinci yayi tsada rayuwa tayi tsanani yan bani na iya sunyi yawa yan kirin kinkin sun karu zaman banza yayi katutu, alal hakika gaskiya daya ce, idan kana son cigaban al’ummarka to ya zama wajibi a kasar nan ka fito ka fadi gaskiya, domacin alumma muke wakilta saboda haka buhari dole ya tsaya ya saurari alumma tare da wakilansu, idan har buhari bai chanza akalar mulkinsa ba wanda intasa gaba bata tsayawa ta waigo baya ba to ya zama lallai mu wakilan alumma mu fito mudauki mataki akan gobnatinnan, apc da pdp duk abu gudane manufa a zahiri shine ke banbantasu. saboda haka buhari shine yafi kowa laifi acikin kasarnan duba da irin halin da ake ciki.
Ahmed yerima dai kafun zamansa dan majalisa ya kasance tsohon dan jarida wanda yayi aiki a voa hausa.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA