Labarin Wani Abokina Da Budurwansa Na facebook da illolin bleaching
Zan so iyaye mata musamman ‘yan mata da zawarawa su samu nutsuwa su karanta wannan rubutun domin zai amfanesu ta fuskar rayuwa
A wannan zamanin, an wautar da hankalin ‘yan mata da zawarawa cewa maza fararen mata suke so, don haka wacce ba fara ba sai ta fara sayen mayukan shafawa masu sa bleaching tana kone fatar jikinta domin tayi haske
‘Yan matan social media, wasun su, suna amfani da application na kwalliya da yake canza musu kalar fatan jikinsu da kyawun fuskarsu, suna yadawa a kafofin sada zumunta domin neman mijin aure ko kuma damfarar garorin samari da fasikai mazinata
Labarin wani abokina, ya hadu da wata budurwa anan Facebook, suka kulla soyayya, sukayi musayen hotuna, yace min ba ta yadda suyi video call domin ya ga asalin fuskarta, kuma a duk lokacin da ya bukaci ta tura masa da hoto ta kan dauki lokaci, sai ya fara fahimtar anya ba Photoshop appl yake gani ba?
A haka dai watarana Allah Ya kaddara tafiya garinsu, bayan ya ziyarci garinsu, ta masa kwatance suka hadu, yace min abinda ya gani a hoton da take tura masa dabam ne da abinda ya gani a zahiri bayan sun hadu, kuma anan ya fahimci dalilin da yasa bata yadda suyi video call
Yace min ta shafe fuskarta da hodar acuci maza, amma yatsun hannunta da kuma kokarin da yayi wajen ganin kafafunta sai ya fahimci cewa bleaching din da takeyi har ya fara bayyana mata illa a jikinta, tun da suka rabu bai sake bibiyarta ba
‘Yan mata ku nutsu ku fahimta, shifa aure ba abune da ake yinsa zuwa wani adadi kayyadadde ba, ana hada aure ne da manufar mutu ka raba, idan kina son more rayuwar aure kar ki yadda namiji ya kaunace ki don surar jikinki ko kalar fatar jikin ki, balle har hakan ya kaiki ga shiga layin mata masu bleaching
A matsayina na Datti Assalafiy, yanzu na doshi shekara 10 da yin aure, don haka ina da ta cewa akan abinda ya shafi rayuwar aure, Wallahi duk wanda ya auri mace don surar jikinta ko don sha’awar jima’i wannan abin zai goshe da zaran sun shekara daya da aure, tuzurai maza da mata ba zasu taba fahimtar haka ba sai sun shiga gidan aure
Saboda haka ina baki shawara ‘yan mata, kar ki yadda namiji ya kaunace ki don ke farace ko don kina da dirin jiki, ki bari namiji ya so ki da aure a yadda Allah Ya halicceki da kuma don kyawun halayenki
Duk abinda ake samu a jikin farar mace akwai shi a jikin bakar mace, kyawun fuska ko kalar fatan jiki wani abune da ido kawai yake gamsarwa
Zaku tausaya ma rayuwar matar da take bleaching idan shekarun tsufa suka fara kamata, abin kyankyami suke dawowa, fatar jikinsu tana yankwanewa, duk tsaftar ta sai tayi wari
Ku dena bleaching, ku zauna a yadda Allah Ya halicceku, shine rufin asirinku, kuma shine jin dadin rayuwar ku na aure a gidan miji, idan ba haka ba, ranar da zakuyi nadama marar amfani yana tafe
Allah Ka sa mata masu bleaching su fahimta su dena.daga shafin Datti Assalafy