Uncategorized

HUKUNCIN AUREN YAHUDU KO NASARA | DR JAMILU YUSUF ZAREWA

Advertisment

HUKUNCIN AUREN YAHUDU KO NASARA


Tambaya :
Malam musulmi zai iya auren ahlul-kitab tana addininta yana musuluncinsa ?


Amsa :
To dan’uwa Allah madaukaki ya halatta auren ahlul-kitabi, wato Yahudu ko Nasara, kamar yadda ya yi bayanin hakan a cikin suratul Ma’ida aya mai lamba ta :
(5),


kuma an samu wasu daga cikin sahabai, sun aure su kamar Usman dan Affan – halifa na uku a musulunci- ya auri Banasariya, haka Dalhatu dan Ubaidillah ya auri Banasariya, sannan Shi ma Huzaifa ya auri Bayahudiya, Allah ya kara musu yarda. duba : Ahkamu-ahlizzimah 2794


Saidai malaman wannan zamanin suna cewa, abin da ya fi shi ne rashin auren Ahlul-kitab saboda yadda zamani ya canza, domin da yawa idan mijinsu musulmi ya mutu yaran suna zama kirista, kai wani wani lokacin ko da sakinta ya yi zata iya guduwa da yaran, sannan zai yi wuya ka samu kamammu wadanda ba su taba zina ba a cikinsu .



Wasu kasashen kuma idan za ka auri kirista daga cikinsu dole zai ka yarda da dokokin kasarsu, a lokuta da yawa kuma za ka samu dokokin sun sabawa ka’idojin musulunci .

Allah ne mafi sani.

  Amsawa

Dr jamilu zarewa
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button