Uncategorized

Hukumar DSS sun kama ‘Osinbajo’ saboda zamba

An kama wani mutumi dake kwaikwayon Osinbajo a Facebook
– An gurfanar da wni mutumi mai shekaru 44, Eseosasere Gift Osifo, a gaban wani babban kotun Osogbo kan zargin kwaikwayon mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo
– Mai shari’ar yace wanda ake zargi ya aikata laifin ne a tsakanin watan Janairu da watan Augusta kafin a kama shi a gurfanar da shi a gaban kotu
Abangaren sa, wanda ake zargi ya karyata laifuka duda biyu da kotu ke tuhumarsa a kai na kwaikwayo da zamba

Hukumar DSS sun zargi wani mutumi mai shekaru 44, Eseosasere Gift Osifo da bude shafin Facebook inda yake amfani da bayanan mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo yana rudar wadanda basu sani ba
Hukumar Department of State Services (DSS) sun kama wani mutumi mai shekaru 44 a duniya, Eseosasere Gift Osifo, kan zargin satar fasaha da zamba.
Jaridar Nation ta bada rahotanni cewa an gurfanar da wanda ake zrgi a gaban wani babban kotun Osogbo a jiya, Alhamis 22 ga watan Satumba, kan laifin bude shafin Facebook da bayanan mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo yana rudar wadanda basu saní вα
A cewar mai hukunci, Mr Onoche Ekwom, babban jami’in doka na hukumar DSS, wanda ake zargin ya aikata laifin ne a tsakanin watan Janairu da watan Augusta kafin a kama shi a gurfanar dashi a gaban kotu.
Ekwon ya fada ma kotu cewa wanda ake zargin yayi amfani da shafin gurin damfarar kudi daga mutanen da basu sani ba a lokuta da dama kafin ya fada a karkon mutun na karshe wanda ya kai ga kama shi.
Mai shari’ar ya ce laifin yayi karo da sashi na 484 da 422 na dokar jihar Osun ta shekara 2002.
A bangarensa, wanda ake zargin ya karyata laifuka guda biyu na satar fasaha da zamba da ake zargin sa a kai.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button