Uncategorized

HUKUNCIN WANDA YA KASHE KANSA DA GANGAN ?

HUKUNCIN WANDA YA KASHE KANSA DA GANGAN ? Tambaya: Assalamu alaik, malam Meye hukunci da matsayin wanda ya kashe kansa ko yai sanadiyyar mutuwarsa da kansa, Allah ya karawa malam ilimi da lafiya. Nagode. Amsa: Wa’alaikum assalam,wanda ya kashe kansa da gangan,ranar Alkiyama zai shiga wuta,zai cigaba da kashe kansa da abin da ya kashe ta da shi a duniya a cikin wutar lahira mai kuna, kamar yadda ya tabbata a hadisi. In har ya mutu da imani ko da kwayar zarra ne, ba zai dawwama a cikin wutar ba, zai fita bayan ya gama lokacin da Allah ya diba masa, kamar yadda hadisai suka bayyana. Allah ne mafi sani. Dr Jamilu Zarewa. 30/5/2016H

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button