An damke matar Nura Murnai, Ƙasurgumin ɗan bindiga a Katsina da naira miliyan 2 a jakan ta


Jaridar PremiumTimes Hausa ta ruwiato Isah ya ce an kama matar Murnai a bisa babur bayan ta dawo daga Kaduna inda ta je harkar karbar kuɗin fansa.
” An kama mai ɗakin Nura Murnai bayan ta dawo daga Kaduna wajen amsar sakon miliyan biyu daga wurin wani abokin harkar mijin ta, Nura Murnai.
” Da aka bincike ta an samu naira miliyan 2 a cikin jakan ta.

Isah ya kara da cewa iata da kanta ta tabbatar wa ƴan sanda cewa ta na yinwa majinta zirga-zirgar amsar kuɗaɗe daga wurare.
Nura Murnai ya shahara wajen satar mutane da harkallar bindigogi wanda ake nema ruwa a jallo.
Ga bidiyon nan kasa ku kalla.



