Labarai

An tura magudun adawar Nijar Hama Amadou gidan yari

Rahotanni daga jamhuriyar Nijar na cewa an kai jagoran adawan ƙasar Hama Amadou gidan yari, bayan ya miƙa kansa ga ‘yan sanda ranar Juma’a.
Kamar yadda Bbchausa na ruwaito.Wata majiya da ke da kusanci da Hama Amadou ta tabbatar da tsare jagoran adawar na Nijar a gidan yari.
Kamfanin dillacin labaru na AFP ya ce an ɗaure Hama Amadou bayan ya sha tambayoyi tsawon kwanaki uku kan zarginsa da hannu a zanga-zangar da ta ɓarke bayan bayyana sakamakon zaɓen shugaban ƙasa.
Ko da yake, zuwa yanzu hukumomi ba su ce komai game da wannan al’amari ba.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button