Uncategorized

Tirkashi: Amarya Ta Tsunduma Tsundum cikin soyayyar mawakin Da Ta Dauko Yayi Mata waka a Wajen Bikinta

Advertisment

Wani abin mamaki ya faru a wajen auren wata budurwa a kasar Amurka

– Budurwar dai mai shekaru 26 ta dauko wani sabon mawaki yayi mata waka

– Kawai sai soyayyar wannan mawaki ta shiga zuciyarta, har ta kai ga ta rabu da mijinta saboda shi

Wata budurwa ta dauko hayar wani mawaki wanda ya girmeta da shekaru 23 yayi mata waka a wajen bikinta, sai dai kuma wani abu da ya faru ya baiwa kowa mamaki, yayin da ta tsunduma cikin kogin soyayyar shi.

Advertisment

Amaryar mai suna Nanny Megan Willis wacce take a garin Baltimore, ta hadu da mawakin mai suna Mark Stone, mai shekaru 49, a lokacin da take birnin New York domin yayi mata waka a wajen bikinta.

Amaryar mai shekaru 26 taje taga ‘yar’uwarta mai suna Kristen, wacce ta dauko hayar Mark domin ya yiwa Megan waka a aurenta da aka yi a shekarar 2016.

Bayan shekara daya yin auren rayuwa ta yiwa Megan wahala, yayin da ta nufi birnin New York domin ta tambayi ‘yar’uwarta dangane da wannan mawaki.

A lokacin da suka je wata mashaya, sai suka hadu da Mark a wajen, inda suka yi ta faman yin hira tare, Mark ya fito ya bayyana mata yadda yayi aure shekaru 27 da suka wuce, a nan dai suka samu fahimtar juna sosai.

Sun cigaba da magana tare har zuwa shekarar 2018 lokacin da Megan ta rabu da mijinta, watanni takwas kawai sai ta bi wannan mawaki garin North Carolina suka hadu a can.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button