Uncategorized

Subhanilillahi : Babu Wata Ribar Azo A Gani A Cikin Aure – Inji Zainab Naseer Ahmad

Advertisment

Yayin da yawancin lokuta iyaye ke Alla-Alla su sanya yayan su mata dakunan mazajen su domin gujewa sharrin zamani da kuma lalacewar tarbiyya, sai gashi wata matashiya mai amfani da yanar gizo da ake Kira Zainab Nasir Ahmad, tace mutane ne kawai ke zuzuta aure kai kace akwai wata babbar nasara a cikin sa, sai dai a zahirin gaskiya wannan tunani shirme ne kawai hasalima babu wani abun azo a gani a cikin sa.

Tace “mutane sai suyi ta zambatar yarinya idan takai matakin aure kuma batayi ba, wannan dalili ne yasa sai kaga wasu mazan ma na tunanin kamar alfarma sukayi miki in suka tunkare ki da zummar aure.”

A cewar ta, “shifa aure abu ne daya kacal na rayuwa, kuma ba kowa ne zaiyi shi ba, tace a gaskuya ya kamata a daina musguna musu akan cewa wai lallai sai sunyi aure.”

Advertisment

Hausaloaded ta ruwaito wannan labari daga Madubi h Ta kuma kara da cewa, ba kuma wai don mace tayi aure hakan na nufin cewa tafi wadanda basuyi bane, duk daya suke.

Daga karshe sai ta kara jaddada cewa ba shakka babu wani abun azo a gani a cikin aure.

Menene ra’ayinku akan hakan?

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button