Uncategorized

Dan shekara 18 ya yi wa kanwar shi mai shekaru 8 fyade a Katsina

r
– An gurfanar da wani matashi mai shekaru 18 a kotu a bisa aikata laifin fyade

– An rahoto cewa yayi ma kanwar sa mai shekaru 8 a duniya fyade

An gurfanar da wani matashi mai shekaru 18 a kotu a bisa aikata laifin yi wa kanwar shi mai shekaru 8 fyade.

Wannan mummunan lamari dai ya faru ne a rukunin gidaje na ‘Steel Rolling Mills’ da ke kan titin Dutsinma a jahar Katsina.

Alkalin Kotun, mai shari’a Hajiya Falile Dikko ta bayar da umarnin a tsare matashin a gidan maza har zuwa ranar 29 ga watan Yuni yayin da za a saurari karar.

‘Yan sanda sun bayyana wa kotun yadda matashin ya yaudari kanwar ta shi zuwa cikin bandaki, inda ya aikata aika aikar akan ta da karfin tuwa.

Tuni aka kai yarinyar asibiti inda aka duba lafiyar ta tare da yi mata magani.

©naij.com

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA