Uncategorized
FATAWAR RABON GADO (92) DR JAMILU YUSUF ZAREWA
Advertisment
FATAWAR RABON GADO (92)
Tambaya
Assalamu Alaikum mallam,mutum ne ya rasu ya bar mahaifiya,mahaifi ya rasu da kanne maza bakwai (7) da mata ukku (3).Yaya rabon gadonsa yake?.Allah ya kara daukaka da fahimta!.
ina nufin mahaifiyarsa tana raye da kanne maza 7 da kanne mata 3 duka uwa daya uba daya.
Amsa:
za a raba abin da aka bari gida shida (6),a bawa uwa kashi daya (1),Ragowar kashi biyar din sai a bawa ‘yan uwan in karfinsu daya a a dangantaka,duk namiji ya dau rabon mata biyu
Allah ne mafi sani
Amsawa :
Dr Jamilu Yusuf Zarewa
posted: by Abubakar Rabiu
Dan Allah ka turawa dan uwanka a Facebook or whatsapp domin shima ya amfana
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com