Uncategorized

HAKKOKI 35 NA MUSULMI AKAN DAN UWANSAMUSULMI.MUNA KULA KUWA? | SHEIK AMINU IBRAHIM DAURAWA

HAKKOKI 35 NA MUSULMI AKAN DAN UWANSA

MUSULMI.
MUNA KULA KUWA?

1 Yayi masa sallama idan sun hadu
2 Yayi masa murmushi da faraa
3, Ya mika masa hannu su gaisa
4, Idan ya kira shi ya amsa
5, Idan BASHI da lafiya yaje ya dubu shi.
6, Idan ana binsa bashi ya taimaka masa wajan
biya
7, Ya dinka kyautata atata masa zato
8, Ya zauna dashi lafiya.
9, Ya bashi abinci idan yana Jin yunwa.
10, Ya girmama dattijo musulmi
11, Ya tausawa yaro musulmi.
12, Ya cika masa alkawari idan sunyi alkawari.
13, Yayi masa sulhu Da wanda suka sami rashin
jituwa.
14, Kada ya dinka tuhumar musulmi.
15, Ya nema masa alfarma idan yana da wata
bukata
16, Ya dinka girmama malamai da masu Ilmi
17, Yayi masa addua idan yayi atshawa
18, Idan ya nemi agajinka ka agaza masa.
19, Ya dinka yi masa addua da fatan alkhairi.
20, Kada ya zalunce shi
21, Kada ya tabar dashi
22, Kada ya dinka yi masa hassada akan wata
niima da Allah yayi masa.
23, Ya girmama shi idan yazo masa a matsayin bako.
24, raka janaizar sa. Idan ya mutu.
25, Ya je kabarinsa domin ziyara da addua.
26, Ya so masa abinda yake sowa kansa
27, kada ya cuci musulmi
28, ya zama Mai tawadiu ga kowa. 29, kada yayi gulmar sa. Ko yayi masa
annamimanci
30, kada ya kaurace masa fiye da kwana uku.
31, Ya kyautatawa dan uwansa musulmi.
32, Kada ya shiga gidansa sai da izninsa
33, Ya umarceshi da kyakyawan halaye ya hanashi mummunan hali.
34, Kada yayi ciniki akan cikinsa.
35, Kada ya nemi aure akan auransa.
36. Kada ya dinka yi masa bincike da bin
diddiginsa.
37, ya kubutar dashi idan yayi rantsuwa.
38, Ya kiyayi mutunci da dukiya da jini na musulmi.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button