Uncategorized
KARATUN ALQUR’ANI, SABODA NEMAN BIYAN BIKATU !|DR JAMILU ZAREWA
Advertisment
Tambaya?
Assalamu Alaikum, Malam ya halatta mu taru muyi karatun Alqur’ani don Allah ya kawo mana sauqi kan matsaloli daban daban?
Amsa :
Wa alaikum assalam, Ya halatta a karanta Alqur’ani ayi tawassuli da shi wajan tunkude bala’o’i, saboda shi karatun aiki ne nagari, kuma aiyuka nagartattu ana iya tsani da su wajan neman biyan bikatu kamar yadda hadisai suka tabbatar.
Anas Dan Malik daga cikin sahabban annabi s.a.w. ya kasance yana tara iyalansa ya yi addu’a Idan ya kammala karatun Alqura’ni, wannan sai ya nuna babu laifi yin hakan, saboda aikin sahabi hujja ne, in ba’a samu wani sahabin ya saba masa ba. Don neman Karin bayani duba Fataawa Arkanil Al-Al-Islam N.a. Ibnu Uthaimin: 354.

Allah mafi sani.
30/10/2016
30/10/2016
DR. JAMILU ZAREWA
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com