Uncategorized
HUKUNCIN BIN SALLAH DAGA LASIFIKA|DR JAMILU YUSUF JAREWA
HUKUNCIN BIN SALLAH DAGA LASIFIKA Tambaya : Malam gidanmu yana kusa da masallaci, muna jiwo kiran sallah da ikama ta lasipika, ko ya halatta in bi sallar jam’i daga laspika ?
Amsa : To ‘yar’uwa wannan mas’alar ta kasu kashi biyu :
1- Idan ya zama dakinki yana like da masallacin, to tabbas wannan ya halatta, saboda nana A’isha ta bi sallar kisfewa rana daga dakinta, a zamanin Annabi s.a.w. kamar yadda Bukhari ya rawaito hakan a hadisi mai lamba ta : 184, sannan Abdurrazak ya rawaito cewa : takan bi ragowar salloli daga dakinta” kamar yadda ya zo a littafinsa na Musannaf a hadisi mai lamba ta : 4883,
saboda dakinta a jikin masallacin yake.
2.idan ya zama dakin ba ya hade da masallacin, to zance mafi inganci shi ne : bai halatta ki bi ba, saboda a zamanin Annabi s.a.w. sahabbai suna haduwa ne a wuri daya ne idan za su yi sallar jam’i, ba sa rarrabuwa, wannan sai yake nuna cewa,
hakan shi ne siffar sallar jama’i, sannan jera sawu a sallah, wani yana bin wani, dole ne . Allah ne masani . Don neman karin bayani duba : Fiqhunnawazil na Khalid Al- mushaikih shafi na : 50
Amsawa
Dr.jamilu zarewa
Dr.jamilu zarewa
BY Abubakar Rabiu Yari
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com
Join Our WhatsApp Channel
Get verified job vacancies, career tips, scholarships and opportunities delivered straight to your phone, free and as soon as they're posted.


