Uncategorized

lafiya: Shisha na dauke da sinadarin da ke haddasa cutar kansa – Rahoton UAE

Wani bincike da ya fito daga UAE, ya bayyana cewa akwai sinadarin karafa da ke haddasa cutar kansa a jikin dan Adam a cikin kayayyakin da ake hada Shisha

Masana kimiyya a Sharjah da Abu Dhabi sun gano cewa medwakh da shisha na dauke da karafan nickel, chromium, copper da kuma zinc – Bincike ya biyo wani nazari da aka gabatar a farkon wannan shekarar, wanda ya bayyana yawan sinadarin nicotine da tar a cikin medwakh, fiye da yadda yake a cikin sigari Wani bincike da ya fito daga hadaddiyar kungiyar daular Laraba UAE, ya bayyana cewa akwai sinadarin karafa da ke haddasa cutar kansa a jikin dan Adam a cikin medwakh da kuma kayayyakin da ake hada Shisha da su, da kuma sigari.

Masana kimiyya a Sharjah da Abu Dhabi sun gano cewa idan aka hadata da sigari, gaba daya sinadarin medwakh da shisha na dauke da karafan nickel, chromium, copper da kuma zinc, masu yawan gaske. Bincike ya biyo wani nazari da aka gabatar a farkon wannan shekarar, wanda ya bayyana yawan sinadarin nicotine da tar a cikin medwakh, fiye da yadda yake a cikin sigari.

 Masana kimiyya suka ce wannan na nuni da cewa masu shan sigari na iya kamuwa da babbar matsaar rashin lafiya da ta hada da cutar kansar huhu da kuma cutar ‘coronary artery’.

 “Medwakh da bututun shisha na dauke na gargajiya basa dauke da abun tacewa, don haka karafa masu hatsari zasu shiga cikin huhu kai tsaye, wanda zai haifar da cututtuka da suka da na huhu da kuma na baki, kamar cutar ‘cardiovascular,” a cewar Ayesha Mohammed, wata lamar ilimin ‘chemistry’ a jami’ar Sharjah, kuma jagorar wannan rahoto.

 “Ba zan taba cewa mutum ya sha dokha [medwakh] da shisa ba saboda basu da mataci, don haka karafa masu hatsari zasu shiga cikin mutum kai tsaye fiye da illar shan sigari, kuma zai haifar da cutar kansa. “Shan medwakh kamar bindiga ce mai cike da harsasai, kuma lokaci ne zai dana kunamar harba ta.

Rahoto daga:hausalegit.ng

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button