Uncategorized

IZNAH PART 5 : Labari Cike Da Makirci

Kuka take sosai har jikinta na kakkarwa sbd rashin sanin takamaimai abinyi Dan kuwa batamasan ya zatayi ta fuskanci gagarumin mur’daden alamarin dake gabanta ba,
Miqewa tayi daqyar rungume da jaririn Sai alokacin taji jibiyarsa da ba’a yankeba tasaka hannunta dake rawa ta lalubo wani ‘dan dutsi Mai tsini ta rintse ido ta yanke zuciyarta na tsinkewa sbd batasan taqamaimai adadin da ake yankewaba.
Gyarasa tayi ta sake shigardashi jikinta ta qanqame tafara laluban hanyar barin gurin cikin tsananin kuka tana waiwayen gawar nafeesa.
Duk inda tasamu ca6a qafarta takeyi cikin tashin hankali da fargaba take ko waiwaye batayi harsaida taga tayi Nisa da gurin ta ‘dan waiwayo hawayen cikin idanuwanta suka gangaro ta Rintse idanu cikin wani irin nauyin zuciya kafin tajuya tafacigaba da tafiya Dan lokacin gab ake da fara Kiran sallar asuba.
Tsayawa yayi tareda zubawa gawar Ido cikin tsananin takaici da baqin cikin mutuwar Tata batareda sunsamu yanda sukeso ba gashi dukkanin alamu sun nuna abinda ta Haifa Yana Raye sbd baya gurin antafi dashi.
Mitssw yaja qaramin tsaki zuciyarsa na tafasa jiyake kamar ya rufe gawar da duka.,
Cikin takaici yakalli Wanda ke kusadashi yace,
Ji9 Kira mum asee.
Waya ya fiddo cikin wandonsa ya dannawa numbernta Kira duk da tsakiyar darene saigashi ta ‘daga Dan ko gigin gifta fuskarta bacci baiyiba bare idanuwanta dake butse qyam da tsananin baqin ciki da 6acin Rai.
Cikin nuna zallar takaicinsa yace,
Matar saheeb ta sheqa lahira….
Wani qaton Abu Mai kamada dutse ya danne maqoshinta tace,
Cikin jikinta fa?
Kallon gawar dake gabansa yayi yana yamutsa fuska yace,
Ta haifesa ba Rai sbd tun Yana ciki na harbesa.
Sai alokacin taji abinda ya tokare numfashinta ya fa’da ta ‘dan saki murya tace,
Good job bullet yanxu ku dauko gawar ku jefar qofar gidan Nan saiku gudu gawar abinda ta Haifa kuwa kusamu jeji ku wullar da shege.
Bullet na kashe wayar ya kalli yaransa yace,
Matuqar mum asee tasanda mun Bari abinda aka Haifa ya tsira to zamu samu matsala Dan itake biyanmu yanda mukeso a aiki Dan haka har abada karwanda yasan abinda ta Haifa na Raye.
Wucewa gaba yayi tareda cewa su biyosa da gawar.
Gudun tashin hankali suka dinga shararawa har suka shigo cikin gari direct anguwar suka nufa daidai gate suka tsaya tareda aje gawar qofar gidan suka koma mota ji9 daya Sanya niqaf da dogon hijab ya qwanqwasa qaton gate din gidan maigadi dake zaune ya rafka uban tagumin tsoro da fargabar haduwarta da saheeb akan 6atan matarsa ya zaburo da sauri ya bu’de gate din cikin fargaba
Saura qiris yayi tuntu6e da gawar yayi saurin ja baya ya zube jiki na rawa daidai Nan ji9 ya shige mota da gudu sukabar gurin.
Hannu biyu Mai gadi ya ‘dora akai Yana salatin daba Kai qarshensa yakeba da qarfi ba inda baya rawa ajikinsa….
Miqewa yayi ya kwasa cikin gida aguje bai tsaya komaiba yahau bubbuga musu qofa hankali atashe.
Abba dake qowarin fitowa sallar asuba yayi saurin qarasowa ya bu’de qofar cikin fargaba
Yana ganin jabiru Maigadi ya fito arikice Yana cewa,
Jabiru lafiya ku……
Gate ya nuna cikin tsananin tashin hankali yace,
Matar oga saheeb ce gatacan awaje wata Mata takawota ta gudu….

Ai abban bai jira sauran bayaninba ya nufi gate din daidai Nan Kamal ya fito da sauri Yana tambayar abba abinda ke faruwa cikin damuwa.
Murmushin gefen baki mum asee dake tsaye bakin windon bedroom dinta dake sama tasaki tareda cewa,
Not bad bullet.,,,
Sbd dabararsu ba laifi tayi Dan yanxu bamai ta6a tunanin maza sukayi aikin za aita bincikene akan mace ce takasheta.
Hmmmnn and I will make sure nikuma Naga na qara lalata tunaninsa  gurin binciken mitswww stupid bastard..
Juyawa tayi tabar bakin windon tareda fadawa toilet ta fiddo spray na pepper tafara fesawa cikin idanuwanta duk da tsananin azabar datakeji kamar zata shide Amma taurin Rai da qarfin baqar zuciyarta ya hanata dainawa
Cikin qanqanin lokaci idanuwanta sukai wani irin mugun kumbura sukai jajir Banda tsiyayar hawayen azaba ba abinda suke daqyar ta it’s alwala ta fito hartayi sallah tagama idanuwanta Basu daina tsiyayar hawayenba.
Kodata idar jiki a sanyaye ta sauko Palo cikin hijab din anan ta tararda Abba da Kamal a tsattsaye sun saka gawar agaba jiki duk a mace ga jabiru gefe Sai sambatu yake sbd nafeesat mutuniyarsace sosai.
Gwaggo Hindu Mai Taya nafeesar Zama tuni ta zube qasa Banda kuka ba abinda takeyi hakama fadime da Deborah masu aiki Suma hawayen suke Dan kuwa suna tsananin qaunarta Dan itace kawai Mai mutumta mutane agidan.
Baya mum asee tayi cikin tsananin tashin hankali tareda sakin saririn kuka tana Kiran sunayen Allah yakurah data fito bedroom dinta tayi saurin tareda cikin damuwa itama.
Waya Abba yafitar tareda barin palon yafara Kiran uwayenta ya sanar musu kafin yakira saheeb Amma Sam wayarsa Bata shiga nandai yakira duk yanuwa da jamaarsa yasanar musu da rasuwar.
Qarfe Tara da rabi na safe suna airport ten jirginsu zai tashi jin sauran thirty minutes din yake kamar basa tafiya.
Wayarsa dake kashe tun jiya ya fiddo tareda kunnawa kamar jira ake saiga Kiran Kamal yashigo wayar
Kallo ‘daya yayiwa screen din ya mayar da wayar sbd badashi yake buqatar wayaba yanxu.
Yana kallo Saida Kamal yayi Masa Kira bakwai kafin ya daina kiran,
Nemo number Abba yayi ya Kira Sai yajisa line busy sai kawai ya sake kashe wayar tareda miqewa riqeda black smiones leather jacket dinsa da iPad da wayarsa dakuma passport dinsa tareda ticket zayyan na gefensa shima Amma waya tunda sukazo yake waya Sai time din ya kashe Yana saka wayar a aljihu tareda gyara zaman jacket dinsa Mai zanen sojoji.
Tunda suka shiga jirgi ya kwantarda kansa tareda rufe idanuwansa Dan he’s having this feeling something is not right.
Zayyan datun a airport Abba yakira yasanardashi jikinsa yake a sanyaye sosai rasuwar ta daki zuciyarsa Dan kuwa yasan tabbas amininsa yayi rashi babba Dan har abada bayasa ran zai Kuma samun maisonsa kamar nafeesat Dan kuwa ta soshi ta qaunaceshi ayanda yake da rayuwarsa da Babu farin ciki ko ka’dan.
Yayita yunqurin sanardashi saiya fasa sbd baimasan ta inda zai fara sanar Masa rasuwarba musamman yanda suka fara ganin haske yafara shigowa duhun rayuwarsa ta sanadin nafeesat da cikinta Amma gashi lokaci ‘daya Allah ya karbi baiwarsa.
Koda jirginsu ya sauka suka fito mota biyu ce tazo ‘daukarsu ‘dayar sojoji ne acike Sai ‘dayar driver ne kawai Kuma shima soldier ne dukkaninsu cikin uniform dinsu suke suna ganinsa suka saurin sunkuyar da kawunansu cikin girmamawa sukace,
Wellcome sir.
Da Kai ya amsa musu tareda shigewa mota Nan take suka bar airport din a guje Dan dama yanada wuya kaga soldiers ba gudu sukeba.
Jabiru dake zaune bakin gate daga waje tareda wasu daga cikin masu gadin kusa dasu dasuka zo gaisuwa Yana hango wutar motocinsu duk da da Rana ne Amma yasan motocin soldiers din oga saheeb kullum akoda Rana a kunne suke ya miqe da sauri yayi ciki ya bu’de gate ‘din gabansa na tsananta fa’duwa.
Lumshe fararen manyan oily eyes dinsa yayi lokacinda yaga harabar gidan da mutane duk da ma tuni wasu suka tafi
Wani sabon nauyi yaji ya qaru a zuciyarsa Akan Wanda yakedashi ya fito ya nufi gurinsu Abba dake jiran qarasowarsa yayi qasa dakai lokacinda wasu Yan uwan nafeesat maza ke Masa gaisuwa.
Shiru yayi batareda ya ‘dagoba har Saida Abba ya dafasa cikin tsananin tausayawa yace,
Allah yaji qanta ya kawo maka sassauci Abdul.
Har magriba ta gabato Yana zaune kusada Abba kansa a sunk
uye still
Ba Wanda baiyi mamaki da jinjinawa jarumta da qarfin hali irin nasaba Dan ko magana bayayi duk Wanda yai Masa gaisuwa Kai kawai yake ‘dagawa idanuwansa sun rine Sai jijiyoyin kansa dasuka firfito ahaka har akai magriba kafin yashiga cikin gida inda ya tararda mum asee ba lafiya sosai Nan dai Dole yasa Kamal Kiran Dr sbd antabbatar Masa da ko ruwa taqi Sha tunda akai rasuwar Nan take tsananin qaunarta da tausayinta yaqara shigarsa  Dan kuwa dan yasan soyayyarta garesa cikin jininta take.
Ana fitowa sallar asuba tafara hango qauyensu maimakon taji sassauci a zuciyarta saitaji hankalinta ya qara tashi gabanta ya tsananta fa’duwa ta tsaya cak tareda ‘dago fuskar jaririn ta kalla hawayen idonta ya gangaro ya sauka har kan fuskarsa ta maidasa jikinta ta rungume ta nufi cikin garin zuwa lokacin gari yafara haske daqyar takai kanta qofar gidansu sbd yanda qafafuwanta sukai Mata nauyi suna hardewa ta tsaya bakin qofar gidan zuciyarta na bugawa da tsanani cikin fargaba da tashin hankali ta cira qafarta daqyar tasa cikin gidan.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button