Kannywood

IBB Tsohon Saurayina Ne ~ Jaruma Ummi Zee Zee

Shahararriyar jarumar fim din Hausar nan mai suna Ummi Ibrahim Wacce akafi sani da Ummi Zee Zee ta tofa albarkacin bakinta akan tsegungumin nan daya daɗe yana yawo akan cewa ta taɓa yin soyayya da tsohon shugaban ƙasa a zamanin mulkin soja wato Janaral Ibrahim Babangida (IBB).

IBB

Ta faru dai ta ƙare, domin kuwa jarumar ta tabbatar da cewa, hakika ta kwashi soyayya da shugaban mulkin sojan.

Idan za’a iya tunawa, shugaban ƙasa Ibrahim Babangida (IBB) ya mulki kasar nan ne daga 1985 zuwa 1993.

ZeeZee

To amma, kalaman na ZeeZee ya biyo bayan tsegungumin ne da ake ta yaɗawa tsakanin mutane da kafafen sada zumunta na zamani cewar ta gina alaƙar soyayya tsakanin ta da tsohon shugaban.

A wata hira ta musamman da jarumar tayi da jaridar Daily Trust, ZeeZee tace, ai tuntuni soyayyar tasu ta tsaya, domin sun daɗe da raba gari. A kalaman ta:

“In gaya muku, tsohon shugaban ƙasa Janaral

Ibrahim Babangida (IBB) saurayina ne, amma mun ɓata yanzu.

 

“Bugu da ƙari, har yanzu abokai ne mu, kuma muna daraja juna. Yanzu haka, ina da saurayi, wanda baya harkar nishadantarwa (harkar Kannywood) kuma shirye-shiryen da mukeyi na auren mu yayi nisa, kuma zamuyi, Insha Allah.
Matar tsohon shugaban ƙasar, Maryam Babangida, a shekarar 2009 ne Allah yayi mata rasuwa, kuma tun daga lokacin Allah bai bashi ikon sake yin aure ba.
To sai dai mai magana da yawun IBB a kafafen yaɗa labarai har yau bai maida martani akan batun yin soyayyar da ZeeZee tayi da tsohon shugaban ƙasar ba, wanda yake uba ga ƙasa.
Kalaman na ZeeZee masu yamutsa hazo, suna zuwa ne a ƴan watanni kaɗan bayan wasu ƴan mata sun fito fili sun bayyana ƴin soyayya da shahararren mai kuɗin nan na Afrika gabaki daya kwata, wato Alhaji Aliko Dangote.inda Majiyarmu ta samu daga jaridar mikiya.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button