Labarai
Rayuwar ƙarya ƴan Nijeriya su ke yi kafin na zo na cire tallafin mai — Tinubu
Advertisment
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce rayuwar ƙarya ƴan Nijeriya ke yi, wacce ta kusa jefa ƙasar cikin bala’in tattalin arziki kafin ya zo ya cire tallafin man fetur a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Tinubu ya ce cire tallafin mai da gyara harkar kasuwancin canjin kuɗaɗe ya zama dole don ceto Nijeriya daga talaucewa.
Tinubu, wanda shugaban jami’ar Ilori, Farfesa Wahab Egbewole ya wakilta, ya fadi hakan ne a yayin bikin yaye dalibai na 34 da na 35 na jami’ar fasaha ta Akure da ke jihar Ondo.
Ya ce gwamnatin sa na sane da radadi da cire tallafin mai da ta yi a kan yan Nijeriya, inda ya kara da cewa gwamnatin ta dauki matakin ne domin dauke basukan da ke kan kasar sakamakon tallafin mai da na Dalar Amurka.
Advertisment