LabaraiUncategorized

Wasu tsirarun ƴan Nijeriya ne ke amfana da tallafin mai kuma gwara da aka cire shi- Ribadu

Advertisment

Mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa cire tallafin man fetur da Shugaba Bola Tinubu ya yi ya kawo karshen safarar man fetur a fadin kasar, kasancewar yan kadan ne kawai daga cikin ‘yan Najeriya ke cin moriyar wannan tallafi.

Jaridar Daily Nigerian Hausa na ruwaito cewa Ribadu ya bayyana hakan a jiya Laraba a Abuja a taron babban kwamandan kwastam (CGCs) da ke gudana a Abuja, inda ya kara da cewa Najeriya tana tallafawa kasashen makwabta ne kawai sakamakon safarar man fetur da ake yi a yankunan iyaka.

“Ni dan yankin iyaka ne kuma kullum sai na samu kira game da yadda kwastam ke tsanantawa masu safarar kaya . Abin mamaki, wadanda ke taimaka musu sun hada da sojoji, amma yanzu komai ya zama tarihi, saboda an canza wadanda ke tallafawa masu safarar man fetur, kuma an maye gurbinsu da sabbin mutane.

“Haka nan kuma, tallafin da muke ta magana akai wanda ya durkusar da NNPC, ba ma yana amfanar da ‘yan Najeriya bane, yana amfanar da kasashen makwabta ne. Muna tallafawa Nijar, Chadi, Burkina Faso, Kamaru, Jamhuriyar Benin, Ghana, da kuma wasu ‘yan Najeriya masu wayo da ke kiran kansu ‘yan kasuwar mai,” inji shi.

Advertisment
Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button