LabaraiUncategorized

RESHE YA JUYE DA MUJIYA: Bayan kotu ta wanke Kwamishina daga zargin kula matar aure, Ƴansandan Kano sun cafke mijin matar

Advertisment

Kwana guda bayan Kotun Shari’ar Musulunci ta wanke Kwamishinan Jigawa Auwal Sankara, daga zargin yin lalata da matar aure, ƴansanda a Kano sun kama Nasir Buba, tsohon mijin wacce ake zargin tana soyayya da kwamishinan, Tasleem Baba-Nabegu.

An kama Buba ne a kofar ofishin lauyan sa a jiya Talata.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa hukumar Hisbah ta jihar Kano kwanan nan ta kama Sankara ta tsare shi bayan Buba ya kai karar cewa kwamishinan na neman matarsa.

Buba ya shigar da kara a kotun Shari’a bisa zargin.

Advertisment

Sai dai a zaman kotun na ranar Litinin, alkalin kotun, Ibrahim Sarki-Yola, ya yi hukuncin wanke Kwamishinan bisa rahoton binciken da ofishin Mataimakin Sufeto Janar na ƴansanda, shiyya ta 1 a Kano ya gabatar.

Ƴansanda sun bayyana cewa bisa bincikensu, ba su samu wani shaidar da za ta tabbatar da zargin zina a kan wanda ake zargi ba.

Bayan kotun ta wanke zargin, sai kuma reshe ya JUYE da mujiya, inda ƴansanda su ka kama mijin matar, Buba, a jiya Talata bisa zargin yi wa matarsa kutse a wayar salular ta.

Majiyoyi sun bayyana cewa Buba ya samo bayanai da dama daga wayar matarsa don yin amfani da su wajen tabbatar da zargin da ya gabatar a kan kwamishinan.

“Gaskiya abin ya nuna cewa ‘yansanda suna da bangaranci a wannan lamari. Nasir ya gabatar da hotuna, bidiyo, saƙonnin rubutu da muryoyi da ke nuna hujjar alakar soyayya tsakanin kwamishinan da matar,” in ji wata majiya da ke da masaniya game da al’amarin.

“Abin mamaki ne yadda ‘yansanda suka wanke kwamishinan sannan suka kama wanda ya kai karar bisa zargin bata suna ta yanar gizo.”

Da aka tuntube shi, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kano, Abdullahi Kiyawa, ya ce ba a sanar da shi wannan ci gaban ba.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button