LabaraiUncategorized

Nollywood ta samu naira biliyan 3.5 daga kuɗin shiga silima a 2024

Advertisment

Masana’antar shirya fina finai ta Nollywood ta cimma wani babban mataki na tarihi, inda ta samu sama da naira biliyan N3.5 daga farkon shekarar zuwa yanzu a gidan sinima na Najeriya.

Wannan ya danganta ne da bayanan da gidan sinima na Najeriya ya fitar, wanda ya kuma bayyana cewa an sayar da fiye da tikiti 935,000. Wadannan alkaluma sun nuna karuwar kashi 125% a kuɗin shiga da kuma kashi 46% a sayar da tikiti idan aka kwatanta da wannan lokacin a bara.

An danganta ingancin samarwa da salon labaran Nollywood a matsayin muhimmin abin da ya taimaka wa masana’antar wajen cimma wannan nasarar tarihi a shekarar 2024.

Tun farkon shekarar, fina-finai da dama suna samun fiye da naira miliyan 100 a gidan sinima, lamarin da ya sa Nollywood kan hanya don cimma shekararta mafi nasara.

Advertisment

Fina-finai irin su Jagun Jagun, Queen Lateefah, Ajakaju, da Farmer’s Bride sun zama manyan fitattun fina-finai a wannan shekarar, inda da dama suka samu fiye da naira miliyan 400 cikin makonni kaɗan bayan fitarsu. Nasarar waɗannan fina-finan ta nuna yadda Nollywood ke ƙara samun damar samar da manyan fina-finai masu jan hankali ga masu kallo iri-iri.

Daily Nigerian Hausa

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button