Labarai

Matsin rayuwa: Zanga-zanga ta ɓarke a Abuja

Advertisment

Yan Najeriya da dama sun taru a Abuja a yau Litinin, suna zanga-zanga game da hauhawar farashin mai, karancin man fetur din da kuma tsananin matsin tattalin arziki.

Jaridar VANGUARD ta rawaito cewa jagororin zanga-zangar su ne Abdullahi Bilal na kungiyar “Gagarumin Gangami na Mutum Miliyan Biyu Don Yaki da Masu Cin Hanci da Rashawa a Harkar Mai”, da Barista Napoleon Otache da Olayemi Isaac daga kungiyar ‘yan gwagwarmayar kare haƙƙin ‘yan ƙasa da ‘yancin tattalin arziki (CEFRAN) a Najeriya, inda su ka nemi a dauki mataki nan take kan abin da su ka bayyana a matsayin gazawar shugabanci wajen kula da bangaren man fetur na kasar.

Babban abin da ya fi jawo hankalin masu zanga-zangar shi ne korafin hauhawar farashin mai da dogayen layukan siye, wanda suka ce yana kara haifar da hauhawar farashin kayayyaki da kuma jefa miliyoyin ‘yan Najeriya cikin talauci.

Masu zanga-zangar sun yi Allah wadai da tsarin tallafin mai na yanzu, suna masu cewa ya zama hanyar da ‘yan tsiraru ke samun riba, yayin da mafi yawan jama’a ke fama da tsadar rayuwa.

Sun bukaci a tsame gwamnatin daga harkokin man fetur baki daya don tabbatar da gaskiya da adalci, da kuma ganin cewa farashin mai ya dace da bukatun jama’a.

Masu zanga-zangar sun kuma yi tir da shigo da man fetur mara kyau, suna masu cewa wannan wata hanya ce ta cin hanci da rashawa da ke cutar da jama’a ta hanyar lalata motocin su da kasuwancin su.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button