Matsalar Tsaro : Shin Da Gaske Barayi Sun Sace Malam Yabo?
Labarin da yake yawo a kafafen yada labarai na jiya da dare barayi sun shiga cikin garin Yabo da ke karamar hukumar mulki da ke kudancin Sakkwato an samu labarin sace malam yabo.
Kalma sace malam yabo ya sanya Mutane sun fara jimaminda firgici cewa an sace malam Bello yabo Sokoto wanda kowa yasan malam Bello yadda yake cacakar yan bindiga da ta’addancin da suke yiwa al’umma wanda har sunyi ta masa barazana, amma malam ko kadan bayajin tsoron su, domin mutum ne wanda idan abu na gaskiya ne ko akan malami,dan siyasa da makamantansu ta fada sai ya fadi domin abu biyu ne mutane ke tsoro gidan yari ko a kashe su.
Ga duk wanda yake saurarin karatun sheikh Bello Yabo yasan cewa ya fadi sam bai tsoron duk wani ɗa da mace ta haifeshi
To Ga asalin labarin.
A karon farko cikin mummunan ayyukan ‘yan ta’addan daji, sun kai hari a garin Yabo da ke Jihar Sokoto inda suka kutsa cikin gidan Malam Abubakar Umar Yabo kuma suka yi awon gaba da shi.
Malam Abubakar Umar Yabo da anka sace ba malam Bello Aliyu Yabo ba, wannan Abubakar umar Yabo matashin malami ne.
Ga hotunasa nan.
Allah Ya yi ma sa mafita, Ya kawo mana ƙarshen wannan bala’i.